Jami’an Tsaro Sun Ceto Jariri ‘Dan Wata 13 Daga Hannun Masu Garkuwa da Mutane

Jami’an Tsaro Sun Ceto Jariri ‘Dan Wata 13 Daga Hannun Masu Garkuwa da Mutane

  • Yayin da ake fama da yawaitar satar mutane, Jami’an ‘yan sanda sun tashi tsaye domin kawo tsaro
  • A makon nan aka ji Rundunar ‘yan sanda na reshen jihar Edo su hallaka ‘yan bindiga a Uhunmwonde
  • Baya ga mutum uku da aka hallaka a gungun masu garkuwa da mutane, an ceto wani jariri da suka sace

Edo - Jami’an ‘yan sandan reshen jihar Edo sun yi nasarar hallaka wasu miyagu a cikin gungun mutane shida da ke yin garkuwa da Bayin Allah.

Tribune ta fitar da rahoto a yau ranar Laraba, 14 ga watan Satumba 2022 cewa ‘yan sanda sun kashe ‘yan bindiga uku a kan titin Benin zuwa Auchi.

Kakakin rundunar ‘yan sanda, ASP Jennifer Iwegbu ta fitar da jawabi dazu tana cewa sun kashe ‘yan bindigan ne a karamar hukumar Uhunmwonde.

Jennifer Iwegbu tace jami’an tsaro sun aukawa ‘yan bindigan bayan sun samu labari daga wata Misis Elizabeth Ojo cewa an yi awon-gaba da jaririnta.

‘Yan sandan sun yi kokari wajen cetowa Ojo jaririnta mai wata 13 da haihuwa. Jami’ar tace an kubutar da jaririn ba tare da ya samu ko kwarzane ba.

Leadership tace wannan yana cikin kokarin dakarun ‘yan sandan na magance satar mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan Sanda
Rundunar 'Yan Sanda Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jawabin ASP Jennifer Iwegbu

“Elizabeth Ojo (mai shekara 42) mazauniyar Achigbor a hanyar Benin-Auchi a karamar hukumar Uhunmwonde a jihar Edo ta kai kuka da kimanin karfe 19:30 a ranar 13/09/2022, tace ‘yan bindiga sun shigo gidanta a Achigbor, hanyar Benin-Auchi a karamar hukumar Uhunmwonde a Edo.
“Nan take jami’an tsaron da ke aiki a nan yankin suka shirya, suka shiga bakin aiki. Da isa gidan da 'yan bindigan suka shiga, Ojo ta fada mana wasu miyagu da ake zagin masu garkuwa da mutane ne, sun yi mata ta'adi, sun dauke jaririnta mai watanni 13 a Duniya, sannan sun shiga jeji da shi.

Ba da bata lokaci ba, jami’ai suka shiga daji domin kokarin ceto jaririn. Masu garkuwa da mutanen suna hango dakarun, suka ajiye jaririn a jeji, suka buda masu wuta. A wajen musayar wuta da ‘yan sanda ne aka ga bayan ‘yan bindiga uku. Ragowar suka tsere cikin dajin.”

Jawabin Kwamishinan 'yan sanda, Abutu Yaro yace har yanzu ana karade jejin. CP Yaro yayi kira ga mutanen Edo suyi hattara a irin wannan lokaci.

Shari'ar takarar PDP

Dazu an samu rahoto da aka je kotu da nufin a cigaba da shari’a tsakanin Atiku Abubakar, Aminu Tambuwal da Nyesom Wike, sai ba a ga Lauya ba.

Prince Michael Ekamon wanda ya shigar da wannan kara a kotu ya fadawa Alkali ciwon ciki ya hana Lauyansa zaman kotu, ya nemi a ba shi lokaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel