Babu Hannun Buhari a Matsalar Rashin Aiki, Laifin Malaman Jami’a Ne Inji Sanatan APC

Babu Hannun Buhari a Matsalar Rashin Aiki, Laifin Malaman Jami’a Ne Inji Sanatan APC

  • Orji Uzor Kalu ya yi jawabi a gaban wasu matasa da aka ware domin a koya masu sana’a a Abuja
  • Shugaban masu tsawatarwa a majalisar kasar ya bayyana abin da ke jawo zaman kashe wando
  • Tsohon gwamnan ya daura laifi a kan malamai, ya wanke shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya

Abuja - Shugaban masu tsawatarwa a majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu ya yi kira ga ‘yan Najeriya su daina zargin shugaban kasa a kan batun rashin aikin yi.

Daily Trust ta rahoto Sanata Orji Uzor Kalu yana cewa ba Muhammadu Buhari ko ‘yan majalisa ne suka jawo ake fama da yawan masu zaman banza ba.

A cewar ‘dan majalisar dattawan, akwai mutane da yawa da aka yaye daga makarantu, ba tare da sun samu isasshen ilmi da ake bukata wajen aiki ba.

Kara karanta wannan

Buhari ya magantu, ya ce akwai wadanda ya kamata suke tallata gwamnatinsa amma ba sa yi

Vanguard tace tsohon gwamnan na jihar Abia ya yi wannan bayani ne a wajen wani taron GST da aka shirya a birnin tarayya Abuja domin a horas da matasa.

Terra Skills suka shirya wannan zama domin a horas da matasa a kan koyon sana’o’i. Sanatan yace shi da Aliyu Sabi Abdullahi suka halarci taron.

Orji Uzor Kalu
Orji Uzor Kalu a taron GST Hoto: @OUKtweets
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu laifinmu ko na Buhari - Kalu

“Ka da mu ga laifin Muhammadu Buhari ko majalisar tarayya a kan yawan marasa aikin yi a kasar nan wanda yake jawo rashin tsaro.
Na taba rike kujerar Gwamna a jiha, saboda haka na san abin da nake magana a kai.
Mafi yawan wadanda suka gama makarantunmu ba su da horo da kyau na yin aiki. Shiyasa ake yawan fama da matsalar tsaro a kasa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali ga 'yan Najeriya yayin da Buhari yace zai haramta amfani da kananzir

Ba laifin shugaba Muhammadu Buhari ko majalisar tarayya ba ne, saboda ba a horas da mutane da kyau wajen harkar shugabanci ba ne."

Sanata ya tsokano malamai

"Zuwa jami’a kadai bai isa ba domin mafi yawan malaman jami’ar nan ba su san abin da suke koyar da ku (matasa) ba.
Na shiga kasuwanci kafin in fara siyasa, na dauki mutane fiye da 13, 000 aiki, saboda haka, na san me nake fada."

Dalibai sun kai Gwamnati kotu

Ana da labari wasu dalibai; Dongo Daniel Davou, Oyebode J. Babafemi, Ejie Kemkanma, Peter Aniefiok da Imam Naziru sun kai gwamnati kotu.

Daliban da kungiyar SERAP sun yi karar Muhammadu Buhari, Chris Ngige da Abubakar Malami, sun bukaci a kawo karshen yajin-aikin ASUU.

Asali: Legit.ng

Online view pixel