ASUU: Wasu Daliban Jami’a Sun Hada-kai, Sun Yi Karar Buhari da Ministoci a kotu

ASUU: Wasu Daliban Jami’a Sun Hada-kai, Sun Yi Karar Buhari da Ministoci a kotu

  • An samu wasu dalibai da suka kai karar gwamnatin tarayya saboda dogon yajin-aikin da ake yi a jamio’i
  • Lauyan da tsayawa daliban yana so shugaba Muhammadu Buhari ya biyawa ‘Yan ASUU duka bukatunsu
  • Kungiyar Socio-economic Rights and Accountability Project (SERAP) tana tare da daliban, ta shigar da kara

Abuja - Kungiyar SERAP da wasu daliban jami’a biyar sun yi karar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a kotu saboda yajin-aikin kungiyar ASUU.

The Guardian ta rahoto cewa wadanda suka shigar da karar sun zargi gwamnatin tarayya da kin biyawa malaman jami’a bukatunsu domin a koma aji.

Lauyan da ya shigar da karar yace gwamnati ta jawo yajin-aikin da ake yi, ya yi tsawo, wanda hakan ya tauye masu hakkin samun ilmi mai nagarta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Na Daf da Asarar Naira Tiriliyan 7.58 Yayin da Ake Ƙarma-Ƙarma

Rahoton yace an hada da Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Dr. Chris Ngige da kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN) a wannan shari’a.

Su wanene wadannan dalibai?

Daliban da suka kai maganar zuwa kotu su ne: Dongo Daniel Davou, Oyebode Joshua Babafemi, Ejie Kemkanma, Peter Itohowo Aniefiok sai Imam Naziru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadannan dalibai suna karatu a jami’o’in OAU, Uni Port, Uni Uyo, UI da jami’ar jihar Filato.

Buhari da Ministoci
Buhari da wasu Ministoci Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Tayo Oyetibo SAN shi ne Lauyan da ya tsayawa daliban, ya shigar da kara mai lamba NICN/ABJ/269/2022 a gaban kotun kwadago mai zama a garin Abuja.

Jaridar Leadership tace Oyetibo SAN ya roki Alkali ya tursasawa shugaban kasa da Ministan kwadago su biyawa ASUU bukatunsu domin a koma karatu.

Lauyoyin SERAP sun je kotu

Kungiyar SERAP mai kare hakkin al’umma tana so a hukunta gwamnati a kan kin cika yarjejeniyar da aka yi a 2009 da kuma alkawarin da aka yi a 2020.

Kara karanta wannan

An Kai Korafi Zuwa Hedikwata, Ana Zargin Shugabannin APC da Satar Milyoyin Kudi

Rahoton yace masu karar sun nemi kotu ta umarci gwamnatin tarayya ta biya malaman jami’a alawus da sauran hakkoki da suka rataya a wuyansu.

Har zuwa yanzu da muke tattara rahoto, ba a sa lokacin da za a saurari wannan kara ba

Gwamnatin Buhari ta je kotu

Dazu aka samu rahoto Shugaba Muhammadu Buhari na neman tursasawa malaman jami’a su koma aiki, an shigar da karar kungiyar 'yan ASUU a kotun NIC.

Mun fahimci cewa ‘tan kungiyar ASUU a Najeriya sun yi tanadin gawurtattun Lauyoyi 46 da za su kare su a kotu, ba tare da an biya su sisin kobo ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel