Wadanda Ya Kamata Su Tallata Gwamnatina Ba Sa Yin Hakan, Inji Shugaba Buhari

Wadanda Ya Kamata Su Tallata Gwamnatina Ba Sa Yin Hakan, Inji Shugaba Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kadan daga nasarorin da ya samu tun bayan hawansa mulkin Najeriya
  • Buhari ya ce akwai wadanda su ya kamata suke fadin irin nasarar da ya samu, amma abin takaici basa fadi
  • Najeriya ta shiga wani yanayi na yawan karbar rancen kudi daga waje tun bayan hawan Buhari a 2015

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Imo - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce akwai wadanda su ya kamata su ke tallata nasarorin da gwamnatinsa ta samu, amma sam ba sa yin hakan, TheCable ta ruwaito.

Buhari ya bayyana haka ne a yau Talata 13 ga watan Satumba a wata ziyarar bude ayyuka da ya kai jihar Imo ta kudancin Najeriya.

Shugaban ya ce, idan aka yi duba cikin tsanaki da irin albarkatun kasa da gwamnatinsa ta samu, za a fahimci irin kokarin da ya yi a mulkinsa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali ga 'yan Najeriya yayin da Buhari yace zai haramta amfani da kananzir

Buhari ya yi tsokaci game da mulkinsa daga 2015 zuwa yanzu
Buhari: Wadanda ya kamata su tallata gwamnatina basa yin hakan | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Da yake tsokaci game da wasu matsalolin da Najeriya ke fuskanta, Buhari ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Game da batun rashin tsaro da ‘yan bindiga, gadar Neja ta biyu, idan ‘yan Nijeriya za su iya tunawa; duk da haka, magana ta gaskiya, ina zargin manyan Najeriya da rashin zama tare da yin tunani mai zurfi game da kasarmu.”

A bangare guda, shugaba Buhari ya kirayi 'yan Najeriya da su yi tunani tare da kwatanta gwamnatinsa da gwamnatocin da suka shude kafin zuwansa.

Abubuwan da gwamnatin Buhari ya cimma, daga bakinsa

Da yake bayyana kadan daga nasarorinsa, Buhari ya ce ya yi aiki tukuru wajen tabbatar da kawar 'yan ta'addan Boko Haram, gina layin dogo da tituna a Najeriya.

A bangare guda, gwamnatin Najeriya a yanzu na cikin wani yanayi na tarin bashi, lamarin dake kara ruruwa wutar martani daga masu sharhi a kasar nan, rahoton People Gazette.

Kara karanta wannan

Atiku ya sha alwashin yin abin da Buhari ya gaza idan aka zabe shi a 2023

Ya zuwa yanzu, ana bin gwamnatin Najeriya bashin akalla N41tr, kuma galibi a karkashin mulkin Buhari aka runtumo bashin.

Hakazalika, gwamnatin a yanzu tana shirin karbo rancen kudin da ya kai N11tr domin tabbatar da tafiyar kasafin kudin 2023 yadda ake so.

Zan Cire Najeriya Daga Kungurmin Duhu Idan Na Gaji Buhari, Inji Dan Takarar PDP Atiku

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sha alwashin fidda Najeriya Najeriya daga kungurmin duhun da take ciki idan aka zabe shi a zaben 2023.

Ya bayyana haka ne yayin da yake magana a wani taron kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Legas (LCCI) ta 2022 da aka yi a Legas, Daily Trust ta ruwaito.

Ya kuma shawarci 'yan Najeriya da cewa, kada su rudu da siyasar farfaganda da barbade a kafafen Facebook, Twitter da Instagram, inda yace hakan ba zai kare su da komai ba.

Kara karanta wannan

'Yan Ta'addan Boko Haram Kasurguman 'Yan Damfara ne, Shugaba Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel