'Yan Majalisa ga Gwamnoni: Motocin da Harsasai Basu Hudawa ba Zasu Kare ku daga Fushin Yaran Talakawa ba

'Yan Majalisa ga Gwamnoni: Motocin da Harsasai Basu Hudawa ba Zasu Kare ku daga Fushin Yaran Talakawa ba

  • Kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai ya shawarci gwamnonin jihohi da su bai wa ilimi fifiko a jihohinsu
  • Shugaban kwamitin, Farfesa Julius, ya sanar da cewa gwamnonin ba zasu kubuta daga fushin yaran talakawa da aka ki ilimantarwa ba
  • Farfesan ya zagaya ayyukan da hukumar UBEC da SUBEB tayi a Kwara inda yake jaddada amfanin ilimantar da yara

Kwara - Kwamitin wucin-gadi na majalisar wakilai kan ilimi a ranar Talata ya ja kunne gwamnonin kasar nan da su fifita ilimi ko kuma su shirya fuskantar kalubale.

Shugaban kwamitin , Farfesa Julius Ihonvbere, ya sanar da hakan a Ilorin, babban birnin jihar Kwara a karshen ziyasar kwana biyu da ya kai na duba ayyukan hukumar UBEC da SUBEB ke yi a jihar.

'Yan Siyasa
'Yan Majalisa ga Gwamnoni: Motocin da Harsasai Basu Hudawa ba Zasu Kare ku daga Fushin Yaran Talakawa ba. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda yace:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano Ta Gana Da ASUU, Ta Bukaci Su Janye Yajin Aiki A Jami'o'in Jihar

"Ina son in shawarci gwamnatocin jihohi da su dauka ilimi da muhimmanci. Motocin da harsasai basu hudawa, karnuka da wayoyin zagaye gidaje ba zasu iya tseratar da su daga fushin yaran da ba a ilimantar ba, wadanda aka ci zarafi da kuma wadanda aka yi watsi da su."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta rahoto, yace ba za a sassautawa duk jihohin da aka kama ba suna waskar da kudaden tallafin UBEC ba.

“Akwai hukunci da aka ware domin jihohin da UBEC ta ware wa manyan ayyuka amma aka yi watsi da su. Muna gyara dokokin UBEC ta yadda zamu karbo wadannan kayyaki kuma mu saka su a hanya domin amfani jama'a.
"Muna neman hanyar tabbatar da an bi doka, lamarin da zai sa jihohi suna da damar samun tallafi amma yin amfani da shi yadda bai dace ba zai fuskanci hukunci."

Kara karanta wannan

Buhari ya magantu, ya ce akwai wadanda ya kamata suke tallata gwamnatinsa amma ba sa yi

- Shugaban yace.

Shugaban kwamitin ya bayyana cewa dukkan gwamnatocin jihohi da suka kiyaye za a saka musu da karin tallafi domin su kara kaimi.

Taraba: Dubban jama'a sun yi wa Nyame maraba bayan Buhari yayi masa rangwame

A wani labari na daban, Jolly Nyame, tsohon gwamnan jihar Taraba a cikin ranakun karshen mako ya samu tarbar girma daga jama'a bayan ya dawo Taraba bayan rangwame da ya samu.

A watan Afirilu, taron majalisar zartarwa ta kasa wacce ta samu jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, ta yi rangwame ga mazauna gidan yari 159 da suka hada da Nyame da Joshua, tsohon gwamnan Filato.

Tsoffin gwamnonin wadanda aka garkame sakamakon damfara, an yi musu rangwame saboda shekarunsu da kuma halin da lafiyarsu ke ciki, TheCable ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel