Gwamnatin Kano Ta Gana Da ASUU, Ta Bukaci Su Janye Yajin Aiki A Jami'o'in Jihar

Gwamnatin Kano Ta Gana Da ASUU, Ta Bukaci Su Janye Yajin Aiki A Jami'o'in Jihar

  • Gwamnatin Jihar Kano ta yi taro da mambobin kungiyar malaman jami'o'i ASUU na jami'o'in jihar biyu a jihar
  • Shugaban ma'aikatan jihar Kano, Usman Bala Muhammad, ya roki mambobin kungiyar su bukaci shugabanninsu su dakatar da su na wata uku don su koma aji
  • A bangarensu, shugaban ASUU na Kano, Abdulqadir Muhammad ya ce da wahala su iya dakatar da yajin aikin idan ba wani abu ya canja bane daga kungiyar ta kasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kano - Gwamnatin Jihar Kano, a yammacin ranar Talata, ta yi taro da mambobin kungiyan ASUU na jami'o'in jiha guda biyu suna neman a dakatar da yajin aiki, Daily Trust ta rahoto.

Rahotanni sun nuna cewa an yi taron ne tsakanin jami'an gwamnati da mambobin ASUU daga Jami'ar Kimiyya da Fasaha (KUST), Wudil, da Jami'ar Yusuf Maitama Sule (YUMSUK).

Kara karanta wannan

‘Dan takara Ya Ba Gwamnati Satar Amsar Magance Matsalar ASUU a Kwana 30

Kungiyar ASUU
Gwamnatin Kano Ta Gana Da ASUU, Ta Bukaci Jami'o'in Jihohi Su Dakatar Da Yajin Aiki. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Taron, wanda aka yi na awanni an tashi ba tare da cimma matsaya ba amma an yi alkawarin za a sake zama cikin sati daya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban ma'aikatan jihar Kano, Usman Bala Muhammad, ya roki kungiyar har ya bukaci mambobin su tambayi shugabanninsu su fita daga ASUU na tsawon wata uku.

Amma, ya bawa kungiyar sati daya su tattauna kan hanyoyin da ya dace - domin a cigaba da karatu a makarantar.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar ya ce:

"Ba zai yi wu ba, ba za mu iya zuwa wurin shugabannin mu na kasa da wannan bukatar ba. Ba za mu iya ba, gara mu fada muku gaskiya."

Da ya ke magana bayan taron kan ko gwamnatin jihar tana shirin daukan mataki kan lakcarorin da ke yajin aiki, shugaban ma'aikatan ya ce a yanzu babu wani shiri a yanzu amma gwamnatin za ta dauki mataki idan abubuwa suka cigaba a hakan.

Kara karanta wannan

A Raba Aurenmu Don Baya Aikin Komai Sai Jajibe-jajiben Fada, Matar Aure Ta Roki Kotu

Ya ce:

"Ba za mu iya korar mutane daga aiki ba sai dai bamu tsari. Ya kamata a tattauna da su domin a ga yadda za a yi sulhu."

Abin da ASUU ta fada wa gwamnatin Jihar Kano

A bangarensa, shugaban ASUU na Kano, Abdulqadir Muhammad, ya ce:

"Mun fada wa gwamnati karara cewa ba za mu dawo mu sake fada musu wani abu daban ba daga bayanin da muka musu sai dai idan wani abu ya canja kafin satin ya kare a matakin kungiya ta kasa.
"Kafin mu fara yajin aikin, ko a hedkwata, mun san abin da zai iya baya, za mu daure idan har ba a warware mana matsalolin mu ba. Yana daga cikin sadaukarwar da muke yi. Idan gwamnati bata fahimci hakan ba, zabin ta ne."

Yajin Aikin ASUU: Ba Dole Ne Sai Kowa Ya Yi Digiri Ba, In Ji Gwamnan APC

A bangare guda, gwamnan Jihar Ebonyi kuma shugaban kungiyar gwamnonin Kudu maso Gabas, David Umahi ya ce ilimin Jami'a fa ba na kowa da kowa bane, rahoton The Punch.

Umahi ya jadada cewa ba adalci bane a yi tsammanin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ciyo bashin fiye da Naira tiriliyan 1 don biyan bukatun ASUU.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164