Taraba: Dubban jama'a sun yi wa Nyame maraba bayan Buhari yayi masa rangwame

Taraba: Dubban jama'a sun yi wa Nyame maraba bayan Buhari yayi masa rangwame

  • Dubban jama'a mazauna jihar Taraba sun yi dafifi tun daga filin jirgin sama na Jalingo domin yi wa Jolly Nyame barka da zuwa
  • Jama'ar sun jeru har zuwa filin wasa na Jolly Nyame dake Jalingo inda suka shiryawa tsohon gwamnan liyafar barka da zuwa
  • An dai yankewa Nyame hukuncin shekaru 12 a gidan maza ne bayan da aka kamashi da laifin waskar da kudaden al'umma har N1.64b

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Taraba - Jolly Nyame, tsohon gwamnan jihar Taraba a cikin ranakun karshen mako ya samu tarbar girma daga jama'a bayan ya dawo Taraba bayan rangwame da ya samu.

A watan Afirilu, taron majalisar zartarwa ta kasa wacce ta samu jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, ta yi rangwame ga mazauna gidan yari 159 da suka hada da Nyame da Joshua, gtsohon gwamnan Filato.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnatin Jihar Kogi Ta Gudanar Da Jana'izar Mutane 130 Da Babu Masu Shi

Tsoffin gwamnonin wadanda aka garkame sakamakon damfara, an yi musu rangwame saboda shekarunsu da kuma halin da lafiyarsu ke ciki, TheCable ta rahoto.

Jolly Nyame
Taraba: Dubban jama'a sun yi wa Nyame maraba bayan Buhari yayi masa rangwame. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

An yankewa Nyame hukunci shekaru 14 a gidan maza a 2018 sakamakon waskar da kudaden al'umma da suka kai N1.64 biliyan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma an rage masa zuwa shekaru 12 a gidan yari a 2020 bayan hukuncin kotun koli wanda ya tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara kan lamarin.

Hukuncin majalisar zartarwar ya janyo cece-kuce inda 'yan Najeriya ke kwatanta hakan da koma baya wurin yaki da rashawa, amma fadar shugaban kasa ta kare kanta.

A watan Augusta, an sako Nyame daga gidan gyaran halin dake Kuje a babban birnin tarayya na Abuja.

A cikin kwanakin karshen mako, tsohon gwamnan Taraba ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Danbaba Danfulani Suntai dake Jalingo a jihar Taraba inda ddubban jama'a suka dinga masa maraba.

Kara karanta wannan

Kwanaki 9 Da Bada Umurnin Damke Ado Gwanja, Safarau Da Yan TikTok 8, Har Yau Ba'a Kamasu Ba

Daga filin jirgin sama zuwa filin wasa na Jolly Nyame, jama'a sun jeru suna maraba da tsohon gwamnan Taraba.

An shirya masa liyafar barka da zuwa wacce aka yi a filin wasa na Jolly Nyame dake Jalingo.

A yayin jawabi a taron, tsohon gwamnan ya mika godiyarsa ga Buhari da majalaisar zartarwa ta kasa wacce tayi masa rangwame.

Amanata Suka ci kuma Suka Karya Alkawari, Wike ya Fallasa Abinda ya Hadasa da Ayu da Atiku

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya yi bayanin dalilin da yasa ya fusata da ‘dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, yace yadda suka kasa mutunta yarjejeniya da alkawurran dake tsakaninsu ne ya fusata shi.

Wike yace Ayu ya sha alwashin yin murabus matukar ‘dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar ya fito daga arewa a maimakon kudancin kasar nan.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Gini Mai Hawa 4 Ya Rushe Ya Fada Kan Mutane Da Dama A Ibadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel