Babu shiga, babu fita: Ma’aikata Za Su Rufe Duka Filayen Tashi da Saukar Jirgin Sama

Babu shiga, babu fita: Ma’aikata Za Su Rufe Duka Filayen Tashi da Saukar Jirgin Sama

  • Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kudirin Civil Aviation Act da Majalisar Tarayya ta aiko masa
  • Sabuwar dokar ta haramtawa ma’aikatan filin jirgi yin bore ko zanga-zanga domin su nuna fushinsu
  • Kungiyoyin ma’aikata irinsu NUATE, ANAP, da AUPCTRE sun fara nuna adawarsu ga wannan dokar

Lagos - Ma’aikatan harkokin jiragen sama sun kammala shirin gudanar da zanga-zanga a duka filayen tashi da saukar jirgin sama na kasar nan.

Rahoton Daily Trust na ranar Alhamis, 8 ga watan Satumba 2022, ya bayyana cewa ma’aikatan suna adawa ne ga sabuwar dokar CAA da aka kawo.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu ga dokar harkar jiragen sama watau Civil Aviation Act wanda za ta karawa Ministan harkokin jirage karfi.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Buhari ya amince a karawa lakcarori wani kason albashi, amma ASUU ta tubure

Tun da wannan kudiri ya zama doka, Ministan tarayya yana da ikon haramtawa kungiyoyin ma’aikata yin zanga-zanga, yajin-aiki ko wani bore.

Kungiyoyi sun yi martani

Ganin ana kokarin murkushe su, kungiyoyin da abin ya shafa suka shirya yakar dokar, sun yi zama da ‘yan jarida a filin jirgin MMIA a Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton yace kungiyar NUATE da ATSSSAN na manyan ma’ikatan da ke aiki a jiragen sama da kungiyar ANAP ta kwararru na adawa da dokar.

Filin jirgi
Shugaban Najeriya a filin jirgi Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Kungiyoyi irinsu NAAPE na masu gyaran jiragen sama da kungiyar hadaka ta AUPCTRE sun yiwa menama labarai jawabin korafinsu a Legas.

Ba za ta sabu ba - Kwamred Aba

Sakataren NUATE na kasa, Kwamred Ocheme Aba ya fadawa ‘yan jarida cewa ba a saurare su a lokacin da ake aiki kan wannan doka a majalisa ba.

Aba yake cewa sabuwar dokar ta haramta zanga-zanga, yajin-aiki ko wani nau’i na dakatar da aiki wanda hakan kokarin ayi masu karfa-karfa ne.

Kara karanta wannan

ASUU: An kai makura, gwamnatin Buhari ta yi sabon batu, ta fadi kokarinta a dinke matsalar ASUU

Babban sakataren na NUATE ya shaida cewa ba za su yi biyayya ga wannan sabuwar doka ba.

Aba yace ma’aikatan zasu fara zanga-zanga a filayen jirgi daga ranar Litinin, idan aka shafe kwanaki 14 ba a dauki mataki ba, to za su daina zuwa aiki.

Yajin aikin ASUU

A baya kun samu rahoto Adamu Adamu wanda ya goyi bayan Kungiyar ASUU a 2013, ya fito yanzu yace Goodluck Jonathan ya jagwalgwala matsalar.

Ministan ilmin yace gwamnatin baya tana sane cewa babu kudi a kasa, amma tayi wa malaman jami’a alkawarin Naira Tiriliyan 1.3 a shekaru shida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel