Don Warware Yajin ASUU, Gwamnatin Buhari Ta Sanar da Karin Albashin Lakcarori da Kashi 23.5

Don Warware Yajin ASUU, Gwamnatin Buhari Ta Sanar da Karin Albashin Lakcarori da Kashi 23.5

  • Gwamnatin Buhari ta kawo tsarin kara albashi ga ma'aikatan jami'o'in tarayya, ASUU ta ce sam ba zai yiwu ba
  • Ministan ilimi Adamu Adamu ya zauna da shugabannin jami'o'in tarayya domin dinke barakar ASUU da gwamnati
  • ASUU ta fara yaji tun watan Fabrairun bana, dalibai sun shafe watanni sama da shida suna zaman kashe wando

FCT, Abuja - A gefen wata tattaunawa, ministan ilimi, Adamu Adamu, yace gwamnati za ta iya kara wa malaman jami'a albashi da 23.5%, yayin da farfesoshi za su samun karin 35%.

Ministan ya bayyan ahakan ne a yau Talata 6 ga watan Satumba a babban birnin tarayya Abuja yayin tattaunawa da shugabannin jami'o'in gwamnatin tarayya, Punch ta ruwaito.

Ministan ya kuma bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi gargadi game da kulla wasu yarjejeniyoyin da gwamnati ba za ta iya dauka ba.

Kara karanta wannan

Yajin Aikin ASUU: FG Na Iya Sauya Hukunci, Zata Biya Malamai Albashinsu da ta Rike

ASUU ta ki amincewa da tayin karin albashin malamai
Don Warware Yajin ASUU, Gwamnatin Buhari Ta Sanar da Karin Albashin Lakcarori da Kashi 23.5 | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Gwamnatin tarayya za ta iya karin 23.5% na albashin ga dukkan ma’aikata a jami’o’in tarayya, in ban da farfesoshi da za su samu karin 35% cikin 100%."

ASUU ta tubure, bata amince da karin ba

Sai dai, minista Adamu ya ce, ASUU da wasu kungiyoyin jami’o’i uku sun ki amincewa da tayin karin na kason da bai kai abin da kungiyoyin suka nema ba, Channels Tv ta ruwaio.

A cewar wata majiya daga ASUU, kungiyar na neman karin sama da 100% na albashi, karin da gwamnatin Buhari tace ba zai yiwu ba.

NASU, SSANU da NAAT tuni sun janye yajin aikin da suke ciki tun bayan samun wata matsaya da gwamnati, ASUU kuwa ta ki amincewa da kowace yarjejeniya.

Idan baku manta ba, ASUU ta fara yajin aikin da ya garkame jami'o'in Najeriya tun ranar 14 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Kafa Kwamitin Da Zai Duba Bukatun ASUU

Ana Batun Yajin ASUU, Jami’ar AUN a Adamawa Ta Dauki Sabbin Dalibai 3,000 Bana, Majiya Mai Tushe

A wani labarin, jami’ar Amurka a Najeriya (AUN) dake Yola, ta ce ta dauki sabbin dalibai sama da 3,000 a tsangayoyi daban-daban da jami'ar ke dashi.

Ya zuwa yanzu dai AUN ce jami'a mai zaman kanta daya tilo dake aiki a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, rahoton Daily Nigerian.

A bangare guda, Jami’ar Khadija Majiya (KUM) ce jami’a mai zaman kanta daya tilo a jihar Jigawa, wacce ke a garin Majia ta karamar hukumar Taura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel