Yan Bindiga Sun Tare Motar Da Aka Dako Gawa Sun Sace Direba Da Mutanen Ciki

Yan Bindiga Sun Tare Motar Da Aka Dako Gawa Sun Sace Direba Da Mutanen Ciki

  • Wasu miyagun yan bindiga sun tare tawagar motoccin da suka dako gawa za su tafi da ita garinsu
  • Maharan sun sace direban motar da ta dako gawar, kanwar matar da ta rasu da wani mutum guda daya
  • Daya cikin yan uwan mammaciyar ya ce sun koma daga bisani sun dako gawar sannan sun sanar da yan sanda

Jihar Abia - Yan Bindiga a ranar Laraba sun tare ayarin motocci da ke dauke da gawa zuwa garin Isuikwuato a Jihar Abia.

Lamarin, a cewar wani majiya daga iyalin, ya faru ne kusa da Ummuneochi/Ihube a babban hanyar Enugu zuwa Port Harcourt.

Taswirar Jihar Abia.
Yan Bindiga Sun Tare Motar Da Aka Dako Gawa Sun Sace Direba Da Mutanen Ciki. Hoto: @VanguardNGA.
Asali: Facebook

Majiya daga iyalan matar da ta rasu ta magantu

Wani cikin iyalan wadanda abin ya faru da su ya shaidawa Vanguard cewa sun taso ne daga Abraka a Jihar Delta lokacin da abin ya faru.

Kara karanta wannan

Rivers: N50,000 Na Siya Kowanne Daga Cikinsu: Rabaren Sista da Aka Kama da Yara 15

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar majiyar, yan bindigan sun tare motar da ke dauke da gawar, suka fito da mutanen da ke ciki suka bar gawar a cikin motar a kan hanya.

Majiyar wacce ta ce gawar matar kawunsa ne, ta ce maharan sun yi awon gaba da mutane ciki har da yar matan, wani cikin yan uwa da direban motar.

Ya ce daga baya yar marigayiyar ta tsere daga hannun maharan yayin da shi kuma direban motan da dayan mutumin suna tsare wurin maharan.

Majiyar wacce ta ce bata son a ambaci sunanta ta ce an sanar da DPO na yan sanda na Isuikwuato saboda a dauki mataki.

Ya ce yan uwan matar da ta rasu sun dako gawar sun mayar dakin ajiyar gawa da ke asibiti.

Kalamansa:

"Hankulan mu sun tashi. An sace mutanen da ke tahowa da gawar matar kawu a Umunneochi zuwa Ihube Okogwe.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka tare hanya a Kaduna, suka kashe mutane da dama

"Sun tisa keyar wadanda suka sace zuwa cikin daji. Mun tafi mun dako gawar kuma sun sanar da yan sanda abin da ya faru. Muna son gwamnati ta tallafa mana."

'Yan Fashi Da Makami Sun Bindige Manjo Na Soja Har Lahira A Jigawa

A wani rahoton, rundunar sojojin Nigeria ta bayyana cewa ƴan fashi da makami sun bindige muƙadasshin kwamandan 196 Battalion, Manjo MS Sama'ila a Dundubus, Jigawa, News Wire ta ruwaito.

A cewar sanarwar da rundunar sojojin ta fitar a ranar Talata, an kashe Sama'ila ne misalin ƙarfe 11.30 na daren ranar Lahadi a hanyarsa ta zuwa Kano daga Maiduguri da mai tsaronsa Alisu Aliyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel