'Yan Ta’adda Sun Tare Hanyar Kaduna, Sun Kashe Mutum 2, Sun Yi Garkuwa da Mutane da Dama

'Yan Ta’adda Sun Tare Hanyar Kaduna, Sun Kashe Mutum 2, Sun Yi Garkuwa da Mutane da Dama

  • 'Yan bindiga sun tare hanya, sun hallaka mutane tare da sace wasu da dama a wani yankin jihar Kaduna
  • Hakazalika, a wani harin na 'yan bindiga sun hallaka wani mutum tare fasa shaguna duk dai a jihar
  • 'Yan bindiga sun addabi yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya, lamarin da ke kara tada hankalin jama'a

Jihar Kaduna - Rahoton da muke samu daga jaridar Daily Trust ya ce, wasu tsagerun 'yan bindiga sun tare hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Rahoton ya ce 'yan ta'addan suka bindige mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu da dama.

Shugaban kungiyar masarautar Birnin Gwari ta BEPU, Ishaq Kasai ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin 5 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

2023: 'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Mutane Wuta a Wurin Taron Jam'iyyar Siyasa, Sun Aikata Ɓarna

'Yan bindiga sun hallaka mutane, sun sace wasu dad ama
'Yan Ta’adda Sun Tare Hanyar Kaduna, Sun Kashe Mutum 2, Sun Yi Garkuwa da Mutane da Dama | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cewarsa,‘yan ta’addan sun hallaka wani direban kasuwa ne tare da sace matafiya da dama dake motarsa, rahoton Punch.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce ‘yan bindigar sun tare hanyar ne tun ranar Alhamis, wacce rana ce ta kasuwa ga jama'ar Birnin Gwari.

A kalamansa:

“Har yanzu ba a bin hanyar. Ya zuwa yanzu, da yawan al’ummomin da ke kan titin kamar su Kwasa-Kwasa, Marabar Kwasa-Kwasa, Nacibi, da Farin Ruwa da dai sauransu duk sun tsere saboda fargabar ko wani abu zai faru.”

Hakazalika, ya ce ‘yan bindigan sun farmaki garin Damari a ranar Asabar da misalin karfe 10 na dare, sun jallaka mutum daya tare da fasa shaguna da dama.

Da yake rokon gwamnati, ya ce akwai bukatar tura jami'an tsaro yankunan Kakangi da Randagi dake makwabtaka.Zamfara da Neja.

Wani Dan Jihar Anambra Ya Harbe Kaninsa Har Lahira Saboda N1,500 Kudin Wutar Lantarki

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Toshe Hanyar Kaduna, Sun Kashe Mutum 2 Tare da Sace Matafiya Da Dama

A wani labarin, kudin wutar lantarki N1,500 ta hada 'yan uwa biyu fada a jihar Anambra, daya ya fusata ya dirkawa daya bindiga.

Peter Orji ya kashe kaninsa mai suna Godwin ne yayin da gardama ta barke tsakaninsu a gidansu dake Uruagu a karamar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar Anambra.

Jaridar Punch ruwaito cewa ’yan uwan biyu suna cikin zaman zamansu ne lokacin da suka fara kai ruwa rana saboda Peter ya ki biyan N1,500 na wuta da yake biya a duk wata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel