N50,000 Na Siya Kowanne Daga Cikinsu: Rabaren Sista da Aka Kama da Yara 15

N50,000 Na Siya Kowanne Daga Cikinsu: Rabaren Sista da Aka Kama da Yara 15

  • Jami'an 'yan sanda a jihar Ribas sun damke wata Rabaren Sista mai suna Maureen Wechinwu kan zargin satar yara 15
  • Duk da ta sanar da cewa siyansu tayi kan N50,000 kowannensu, an gano cewa sato su aka yi daga jihohin kudu
  • A cewartsa, gidan marayu gareta inda take kulawa da yaran mahaukata amma ana kawo mata yaran siyarwa tana siya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rivers - Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Ribas sun damke wata da ake zargi da safarar yara mai suna Maureen Wechinwu wacce tayi ikirarin ita Rabaren Sista ce kuma siyan yaran tayi.

'Yan sandan dogaro da bayanan sirri sun cafke Maureen a gidanta dake Aluu, karamar hukumar Ikwerre ta jihar Ribas kuma sun ceto yara 15 daga gidan, jaridar Vanguard ta rahoto.

'Yan sanda
N50,000 Na Siya Kowanne Daga Cikinsu: Rabaren Sista da Aka Kama da Yara 15. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Friday Eboka, ya bayyana cewa an ceto yaran masu shekaru bakwai zuwa tara inda ya kara da cewa za a gurfanar da wacce ake zargi bayan kammala bincike.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Tribune Online ta rahoto cewa, Eboka yace binciken farko ya nuna cewa an sato yaran ne daga sassa daban-daban na jihohin kudu kudu kuma aka siyar da su.

Yace sai da suka kwashe sama da sa'o'i 24 kafin yaran su iya bayyana abinda suke fuskanta ga 'yan sanda inda ya kara da cewa an azabtar da su ba kadan ba.

Ya ce:

"A ranar 3 ga watan Satumba, jami'an rundunar da suka yi aiki da bayanan sirri kan maboyar yaran da aka sace sun dira a Omuigwe Abuja Phase II, Aluu dake karamar hukumar Ikwerre.
"An kama wata budurwa mai suna Maureen Wevhinwu mai shekaru 44 dake ikirarin ita Rabaren Sista ce.
"An ceto yara 15 kuma an mika lamarin hannun sashen kula na kwamishinan 'yan sanda domin binciken tsanaki."

Na yi abun kunya, wacce ake zargi tace

Maureen Wechinwu, a wata tattaunawa da aka yi da ita tace ta ba jama'a kunya da kuma kanta inda ta jaddada cewa bata safarar yara.

Maureen tace:

"Ina da gidan marayun da nake rike yaran mahaukata. Fransisca Onyinyechi, wacce wata mahaukaciya a wurin kasuwar Ogbogoro ta haifa tana daya daga cikinsu.
"Ba zan iya cewa ni rabaren sista bace yanzu saboda abun kunyar da nayi. Amma da farko na yadda ni ce."

Ta kara da cewa:

“Ina aiki da Ladies of Victory Missionary Sisters dake Ingila. Ni kadai ce 'yar Najeriya a ciki. Wasu daga cikin yarana 'ya'yan mahaukata ne. Sauran kuwa na siye su ne daga wurin wani Victor.
“A wasu lokutan ya kan kawo min biyu. Wata Alice ta kawo min biyu. Tace tunda yanzu na fara in dauke su.
“A wasu lokutan idan Victor ya kawo min yaran, ya kan karba kudi. Amma saboda matsin da nake ciki na kan ba shi N50,000, N60,000, ko N100,000

Asali: Legit.ng

Online view pixel