'Yan Bindiga Sun Rike Mutumin da Ya Kai Kuɗin Fansar DPO, Sun Aike da Sako
- Yan bindiga sun yi garkuwa da wanda ya tafi kai kudin fansa miliyan Bakwai domin kuɓutar da DPOn yan sanda a Kaduna
- Wasu bayanai sun ce ɗan sandan na cikin mawuyacin hali a hannun yan ta'adda, ruwan sama na dukan shi ga azabtarwa
- Kusan watanni biyu kenan da aka sace ɗan sandan a kan hanyarsa ta zuwa Birnin Gwari domin kama aiki
Kaduna - 'Yan ta'addan da suka yi garkuwa da DPO na hukumar yan sanda a kan hanyarsa ta zuwa kama aiki a Birnin Gwari, jihar Kaduna, sun yi barazanar kashe shi idan ba'a biya musu buƙatunsu ba.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa sun yi barazanar kisan ne bayan sun riƙe wanda aka tura ya kai musu Miliyan N7m kuɗin fansar da iyalan DPO da abokanan arziki suka haɗa.
Wata majiya da ta zanta da BBC Hausa ranar Litinin tace Iyalai da abokan arzuki ba zasu iya cika buƙatun 'yan ta'addan ba, sun yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni su taimaka musu.
A cewarsa, "Da farko sun nemi miliyan N250m, mun faɗa musu bamu da hanyar waɗannan kuɗin. Mun tattauna da 'yan uwa da abokanan kwarai, aka tattara miliyan N5m aka baiwa yan ta'adda."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Bayan sun dafe kuɗin sai suka gaya mana na ciyarwa ne mu sake tara musu miliyan biyu na sanya Kati da Babur. Haka a daddafe muka sake tara kuɗin muka tura musu, wanda yaje kai kudin bai dawo ba."
"Har yanzun DPO na nan a raye amma yana kashin jini yayin da suka barshi ruwa na bugun shi, sun ɗaure shi da sarka, kullum rokon mu yake mu taimaka mu kubutar da shi."
Muna bukatar taimako ba abinda zamu iya
Mutumin ya ƙara da cewa lamarin na bukatar taimakon gaggawa, inda ya yi kira ga gwamnati ta tallafa wa iyalan DPO cikin sauri domin kuɓutar da shi daga hannun maharan.
"Ba abinda zamu iya yi game da lamarin a halin yanzu karfin mu ya ƙare, ba zamu iya tattara kuɗin da suke buƙata ba."
A wani labarin kuma FG ta bayyana cewa ta ci karfin matsalar tsaron Najeriya amma har yanzu akwai sauran yaƙi
Gwamnatin shugaba Buhari tace Sojoji da sauran hukumomin tsaro na samun nasara a kokarin dawo da zaman lafiya a Najeriya.
Ministan labarai, Lai Muhammed, ya ce duk da akwai sauran yaƙi amma za'a iya cewa an magance mafi munin matsalar.
Asali: Legit.ng