Wani Rahoto Ya Bankado Yawan Bindigun Dake Hannun Mutane a Najeriya

Wani Rahoto Ya Bankado Yawan Bindigun Dake Hannun Mutane a Najeriya

  • Wani Rahoto da aka bayyana ya nuna cewa akwai bindigu sama da miliyan Shida a hannun 'yan Najeriya
  • Wannan na zuwa ne duk da namijin kokarin da gwamnati tace tana yi na dakile yaɗuwar makamai ba bisa ƙa'ida ba
  • Hukumar 'yan sanda ta kasa tace kwata-kwata rahoton bai da inganci domin sun kwato makamai hannun 'yan ta'adda da yawa

Wani rahoton Fasaha da SBM Intelligence suka fitar ya nuna cewa akwai aƙalla bindigu miliyan 6,154,000 dake yawo a hannun fararen hula a sassan Najeriya.

Punch tace rahoton SBM ya ƙunshi cewa Bindigun sun kai kashi 3.21 a duk mutum 100, yayin da addin bindigu dubu 224,200 ke hannjn rundunar sojoji da wasu 362,400 a hannun sauran hukumomin tsaron Najeriya.

An jingina yawaitar kananan makamai da yaɗuwar matsalar tsaron kasar nan, duk da faɗi tashin da gwamnati ke yi na ganin ta ɗaƙile lamarin a lokuta da dama.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku Abubakar da Gwamna Wike Sun Amince da Bukata Ɗaya Kafin Fara Kamfen 2023

Sufeta Janar na yan sand, IGP Usman Baba.
Wani Rahoto Ya Bankado Yawan Bindigun Dake Hannun Mutane a Najeriya Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Daga cikin irin hoɓɓasa da gwamnatin tarayya ta yi har da amince wa da kafa sabuwar cibiyar kula da ƙananan makamai, da zummar dakile yaɗuwarsu a cikin al'ummar ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma, majalisun tarayya sun amince da kudurin dokar kafa hukumar kula da kananan makamai da magance yaɗuwarsu tsakanin mutane ta ƙasa. Amma har yanzun shugaban kasa bai rattaɓa haannu a kai ba.

Wace rawa hukumar zata taka idan shugaban kasa ya sanya hannu?

A cewar wani shafin Intanet 'Legal Advocacy Centre" idan shugaban kasa ya rattaɓa hannu aa kudirin, zai bai wa hukumar damar zama kungiya mai zaman kanta, kuma hakan zai bata damar aiki yadda ya kamata.

Duk wani yunƙurin domin jin ta bakin kakakin shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu, bai kai ga nasara ba domin ya ƙi amsa tambayoyin da aka aike masa kan batun har zuwa lokacin da muka haɗa wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Fallasa Wanda Wike da Wasu Gwamnoni Suka Amince Ya Gaji Buhari a 2023

Wani masani kan harkokin tsaro, Timothy Avele, ya ce akwai bindigu a hannun mutane sama da yawan adadin da aka bayyana a cikin rahoton.

Ya kuma nuna shakku kan cewa ko da shugaban ƙasa ya rattaɓa hannun kan kudirin kafa hukumar, ba tabbas bane a samu wani banbanci.

Avele yace:

"A ganina wannan bai haɗa da makaman da yankuna suka mallaka ba da wasu da ba'a san da su ba. Babu ɗaya daga cikinsu da zai nuna banbanci na a zo a gani matukar mazauna na jin barazana da rashin tsaro."
"Abun takaici ne yadda cin hanci ya mamaye iyakokin ƙasa da na ruwa wanda ya saukaka safarar irin waɗan nan kayayyaki masu haɗari zuwa cikin ƙasa.
“Kada ku manta cewa ana ƙera wasu makaman a cikin kasa amma ba'a ɗaukar matakan fasaha da nufin tarwatsa masu kera su da samar da tabbacin tsaro babu abin da zai yi tasiri."

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu Ya Magantu Kan Rikicin Atiku da Wike, Ya Raɗa Wa PDP Sabon Suna

Haka zalika, wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Dickson Osajie, yace adadin bindigun da aka gano hannun mutane wata alama ce dake nuna hadari ga kasar nan wacce ke shirin gudanar da babban zabe a 2023.

Ya hukumar yan sanda ta ji daa rahoton?

A ɓangarensa, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana rahoton a matsayin wanda bai inganta ba.

“Game da wannan lamari, ba zan ce rahoton na gaske ba ne domin babu mutum ɗaya da ya san yawan makaman dake hannun gurɓatattun mutane. Haka nan bana tunanin alkaluman da aka ambata su zama gaskiya saboda mun kwato wasu."

- Olumuyiwa Adejobi.

Jami'in ɗan sandan ya kara da cewa hukumomi masu ruwa da tsaki kan lamarin suna iya bakin kokarinsu wajen daƙile safara da yawaitar ƙananan makamai kuma basu tunanain adadin zai ƙaru nan gaba.

A wani labarin kuma Sojojin Najeriya Sun Kashe Mayakan Boko Haram 200 Da Manyan Kwamandoji 5

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamna Wike Ya Yi Barazanar Taimaka Wa Atiku Ya Sha Kaye a Zaben 2023

Mayakan Boko Haram sun sha kashi a hannun dakarun sojojin Operation Hadin Kai inda suka halaka mayakan kungiyar guda 200 ciki harda manyan kwamandojinsu guda biyar a yankin dajin Sambisa.

Dakarun sojojin sama da suka hada da bataliya ta 199 da ta 222 sun kaddamar da hare-haren ne a ranar 1 ga watan Satumban 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel