Kaduna: 'Yan Sanda Sun Yi Ram da Mutum 3 Dake Kaiwa 'Yan Bindiga Bayanan Sirri

Kaduna: 'Yan Sanda Sun Yi Ram da Mutum 3 Dake Kaiwa 'Yan Bindiga Bayanan Sirri

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da kama wasu matasa uku da zargin kai wa 'yan bindiga bayanan sirri a Rigachikun da Maraban Jos
  • Hafsat Ibrahim da Rabi Bala suna soyayya da 'yan bindigan ne kuma suna taimaka musu wurin kaiwa da kawowa da makamansu
  • Shi kuwa Bayero Adamu ya sanar da cewa yana kai musu bayanai wanda da hannunsa a manyan farmakin kan hanyar Kaduna zuwa Zaria

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna tace ta damke wasu mutum uku a Maraban Jos da Rigachikun a karamar hukumar Igabi ta jihar kan zarginsu da kai wa 'yan bindiga bayanan sirri.

Wadanda ake zargin an gano sunayensu da Hafsat Ibrahim, Rabi Bala da Bayero Adamu dukkansu matasa kuma sun shiga hannun 'yan sintirin jihar dake aiki a yankunan kwanaki biyu da suka gabata, sannan an mika su hannun 'yan sandan domin cigaba da bincike.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kwashe Matafiya 32 Dake Dawowa Daga Jana'iza a Ondo

Yan Bindiga
Kaduna: 'Yan Sanda Sun Yi Ram da Mutum 3 Dake Kaiwa 'Yan Bindiga Bayanan Sirri. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa, a yayin tabbatar da kamen, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, yace dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifukansu.

Kamar yadda ya tabbatar, 'yan matan biyu suna soyayya ne da 'yan bindigan kuma suke taimaka musu wurin samun kaiwa da kawowa da makamai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Dayan namijin ya amsa cewa ya taka rawar gani tare da wasu 'yan kungiyar ta'addancin wurin aiwatar da miyagun hare-hare a kan babban titin Kaduna zuwa Zaria da yankuna masu makwabtaka da nan, amma ana cigaba da bincike," yace.

Katsina: 'Yan Sanda Sun Cafke Masu Kaiwa 'Yan Bindiga Bayanai, Sun Fadi Irin Barnar da Suke yi

A wani labari na daban, tawagar binciken sirri ta IRT dake karkashin sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, ta damke mai kai wa 'yan bindiga bayanan da ya kia ga sace mata da 'ya'ya biyu na Ibrahim Aminu, 'dan majalisa a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 3 A Jihar Borno

Rundunar IRT tabayyana hakan a takardar da ta fitar a ranar Lahadi daga sakateriyarta, TheCable ta rahoto.

'Yan bindiga sun kai farmaki gidan 'dan majalisar dake wakiltar mazabar Bakori a majalisar jihar Katsina kuma suka yi awon gaba da matar da yara biyu a watan Satumban 2021, shekara daya bayan garkuwa da shi da aka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel