Mayakan Boko Haram Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 3 A Jihar Borno

Mayakan Boko Haram Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 3 A Jihar Borno

  • Mayakan Boko Haram sun farmaki al'umman Ngulde da ke karamar hukumar Askira-Uba a jihar Borno
  • Mummunan harin da kungiyar ta'addancin ta kai ya yi sanadiyar mutuwar babban limamin Gima da wasu mutane uku
  • Maharan sun kuma sace kayan abinci da dabbobi tare da lalata dukiyoyi na miliyayin nairori

Borno - Akalla mutum hudu ne suka mutu ciki harda babban limamin Gima, sannan wasu da dama sun jikkata yayin da mayakan Boko Haram suka farmaki garin Ngulde da ke karamar hukumar Askira-Uba ta jihar Borno.

Mayakan sun kuma sace dabbobi da kayan abinci ba tare da cikas ba, bayan sun cinnawa motoci biyu wuta, kasancewar Ngulde garin manoma ne da ke a wani bangare na dajin Sambisa.

Sojoji
Mayakan Boko Haram Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 3 A Jihar Borno Hoto: dailynigerian.com
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa yan ta’addan da yawansu ya fi 20 dauke da Muggan makamai da bindigogi sun farmaki garin ne tun a ranar Juma’a sannan suka yi barna.

Kara karanta wannan

Ruwa Yayi Awon Gaba da Sama da 'Yan Boko Haram 70 Sakamakon Luguden Sojojin Najeriya

Sai dai kuma, rashin kyawun hanyar sadarwa a yankin ya kawo tsaiko wajen samun bayanai game da mummunan harin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kansila da ke wakiltan unguwar Ngulde, Hon. Bilyaminu Umar ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook a safiyar ranar Lahadi.

Umar ya ce lamarin wanda ya afku a ranar Juma’a 2 ga watan Satumba bayan sallar Asubahi ya yi sanadiyar mutuwar mutum hudu sannan da dama sun jikka.

Ya kuma bayyana cewa maharan sun lalata tare da sace kayayyaki na miliyoyin nairori.

Ya kuma tausayawa wadanda abun ya ritsa da su yayin da ya yi kira ga gwamnati da ta samar da kayan agaji ga mutanen da abun ya ritsa da su don saukaka wahalar da suke ciki.

Ya ce:

“Tuni na sanar da mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Borno, Injiniya Abdullahi Askira game da wannan mummunan hari, ya yi alkawarin gabatar da shi ga Farfesa Babagana Umara Zulum don daukar matakan da suka dace.”

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC Ta Kama 'Yahoo Boys' 41 Da Dukiyoyin Da Suka Mallaka

A wata hira da mamba mai wakiltan Askira-Uba, wanda ya kasance mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Borno, Rt. Hon Abdullahi Askira, ya tausayawa wadanda abun ya ritsa da su.

Ya kuma yi addu’an samun lafiya ga wadanda suka samu raunuka ta sanadiyar harbi a harin.

Yayin da yake addu’an Allah ya jikan wadanda suka rasu, kakakin majalisar ya bukaci iyalansu da mutanen gari da su yi dangana, domin an sanar da gwamnati da hukumomin tsaro don hana sake afkuwar hakan.

Ruwa Yayi Awon Gaba da Sama da 'Yan Boko Haram 70 Sakamakon Luguden Sojojin Najeriya

A wani labarin kuma, sama da mmutum 70 da ake zargin 'yan Boko Haram ne ruwa yayi awon gaba da su a a wani rafi bayan luguden wutan da dakarun Operation Hadin Kai suka yi a jihar Borno, majiyoyi suka tabbatar.

An tattaro cewa, sojojin Najeriya tare da hadin guiwar kungiyar tsaron farar hula, JTF, sun halaka sama da 'yan ta'addan Boko Haram 20 a kauyen Sheruri dake karamar hukumar Bama ta jihar Borno a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wani kasurgumin dillalin bindiga dauke da makamai zai tafi Zamfara

Majiyoyi sun ce bayan farmakin Sheruri, wadanda suka tseren ruwa yayi awon gaba da su a rafin dake kusa da kauyen Dipchari dake karamar hukumar Bama a ranar Juma'a, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel