Katsina: 'Yan Sanda Sun Cafke Masu Kaiwa 'Yan Bindiga Bayanai, Sun Fadi Irin Barnar da Suke yi

Katsina: 'Yan Sanda Sun Cafke Masu Kaiwa 'Yan Bindiga Bayanai, Sun Fadi Irin Barnar da Suke yi

  • Rundunar IRT ta kama wasu mutum 3 da ake zargi da kai wa 'yan bindiga bayanan sirri a Katsina wanda ya kai ga sace mata da 'ya'yan 'dan majalisa
  • Kamar yadda daya daga cikinsu mai suna Muttaka Ibrahim ya sanar, ya samu N130,000 daga wurin Sanni Tukur, fitaccen shugaban 'yan bindiga
  • 'Dan majalisar mai wakiltar mazabar Bakori, Ibrahim Aminu, yace sai da ya lale N37,500,000 sannan aka sako matarsa da 'ya'yansa biyu

Katsina - Tawagar binciken sirri ta IRT dake karkashin sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, ta damke mai kai wa 'yan bindiga bayanan da ya kia ga sace mata da 'ya'ya biyu na Ibrahim Aminu, 'dan majalisa a jihar Katsina.

Rundunar IRT tabayyana hakan a takardar da ta fitar a ranar Lahadi daga sakateriyarta, TheCable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karfin hali: An kama wani sojan bogi da ke yiwa mata fashi da makami

IRT Team
Katsina: 'Yan Sanda Sun Cafke Masu Kaiwa 'Yan Bindiga Bayanai, Sun Fadi Irin Barnar da Suke yi. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

'Yan bindiga sun kai farmaki gidan 'dan majalisar dake wakiltar mazabar Bakori a majalisar jihar Katsina kuma suka yi awon gaba da matar da yara biyu a watan Satumban 2021, shekara daya bayan garkuwa da shi da aka yi.

Jami'an IRT dake aiki da Operation Restore Hope, sun ce sun yi aiki da bayanai gamsassu kuma suka kama wadanda ake zargin a maboyarsu daban-daban.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan wadanda ake zargin sune Muttaka Ibrahim, Sulaiman Rabi'u da Surajo dukkansu maza kuma 'yan asalin karamar hukumar Bakori. An kama su kan zarginsu da ake yi da samar da bayanan sirri da suka kai ga garkuwa da iyalan 'dan majalisar.

Kamar yadda takardar ta bayyana, Muttaka Ibrahim ya amsa laifinsa kuma ya karba N130,000 daga shugaban 'yan bindigan sannan yace Yusuf Bala dake Zaria ne abokin aikinsa.

Ibrahim yace shi da sauran mambobin tawagarsa ne masu kai wa Sanni Tukur bayanai wanda aka fi sani da Abacha, wanda ya kware wurin addabar mazauna jihohin Katsina da Zamfara.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Magantu Kan Batun Kama Bakin Haure Suna Dillancin Makamai da Helikwafta

A yayin bayanin abinda ya fuskanta ga 'yan sanda, 'dan majalisar yace ya biya N37,500,000 ga shugaban 'yan ta'addan domin karbar iyalinsa.

'Yan Sanda Sun Cafke Sojojin Bogi 2 a Legas Dauke da Layu da Makamai

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Legas tace ta cafke wasu sojan bogi biyu a jihar. Kakakin rundunar 'yan sandan, Benjamin Hundeyin, yace an same shi da kayan sojoji, 'yan sanda, layu da harsasai masu rai.

A wata takarda da ya fitar, Hundeyin yace Oluwatosin Gabriel, daya daga cikin wadanda ake zargin, ya shiga hannu ne yayin da ake dabbaka dokar haramcin yawon babura a wasu sassan jihar, TheCable ta rahoto.

Yace 'yan sanda suna binciken kwakwaf wanda hakan ya kai ga kama Nurudeen Agboola, wanda ake zargi na biyu wanda shi ke samar da kayan sojojin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel