'Yan Bindiga Sun Kwashe Matafiya 32 Dake Dawowa Daga Jana'iza a Ondo

'Yan Bindiga Sun Kwashe Matafiya 32 Dake Dawowa Daga Jana'iza a Ondo

  • Miyagun 'yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya 32 a yankin Ifon dake karamar hukumar Ose ta jihar Ondo
  • An gano cewa, matafiyan suna dawowa ne daga jihar Edo inda suka halarci wani bikin mutuwa a ranar Asabar
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta sanar da cewa an ceto mutum daya wanda a halin yanzu yake bada muhimman bayanai don ceto sauran

Ondo - Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun yi awon gaba da matafiya 32 a wuraren Ifon dake karamar hukumar Ose ta jihar Ondo.

Wadanda aka sacen an gano cewa suna dawowa ne daga bikin mutuwa da suka yi a jihar Edo a ranar Asabar lokacin da lamarin ya faru, jaridar Vanguard ta rahoto.

Maharan
'Yan Bindiga Sun Kwashe Matafiya 32 Dake Dawowa Daga Jana'iza a Ondo. hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Har yanzu ba a tabbatar da cewa ko masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan wadanda suka sacen ba domin biyan kudin fansa.

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 3 A Jihar Borno

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ondo, SP Funmilayo Odunlami ta tabbatar da garkuwa da jama'a a zantawar wayar salula da tayi da Channels TV.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Odunlami ta bayyana cewa an ceto daya daga cikin mutanen a halin yanzu kuma yana bai wa 'yan sanda bayanai masu muhimmanci a kan lamarin duka a kokarin ceto sauran.

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallacin Juma'a a Zamfara, Sun Kwashe Jama'a

A wani labari na daban, 'yan bindiga a ranar Juma'a sun sace masallata masu tarin yawa daga Masallacin Juma'a na yankin Zugu dake karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun ce 'yan bindigan sun boye bidigoginsu a cikin kayansu kuma suka shiga masallacin yayin da liman yake dab da fara huduba, Daily Trust ta rahoto.

Maharan sun sanar da wadanda ke wajen Masallacin da su shiga ciki.

Kara karanta wannan

Ruwa Yayi Awon Gaba da Sama da 'Yan Boko Haram 70 Sakamakon Luguden Sojojin Najeriya

"A lokacin da suka zagaye masallacin, sun bukaci duk wadanda ke wajen masallacin da su shiga ciki cewa sun zo ne domin tattauna kan yadda zasu sako wasu mutanen dake hannunsu.
"Babu wanda ya gansu da bindigogi kuma mutane da yawa sun kallesu a matsayin masu bauta. Babu wanda ya mayar da hankali kansu saboda sun boye bindigoginsu.
"Sai dai, jim kafdan bayan sun shiga cikin masallacin suka fito da bindigoginsu tare da yin harbin gargadi," mazaunin yankin ya tabbatar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel