'Yan Sanda Sun Yi Gumurzu da Yan Bindiga, Sun Ceto Dan Takarar PDP a Katsina

'Yan Sanda Sun Yi Gumurzu da Yan Bindiga, Sun Ceto Dan Takarar PDP a Katsina

  • Gwaraazan jami'an yan sanda a jihar Katsina sun kubutar da ɗan takarar kujerar majalisar jiha karkashin inuwar PDP a Kankiya
  • Mai magana da yawun yan sanda, SP Gambo Isah, ya tabbatar da nasarar bayan gumurzu da maharan da daren Asabar
  • Haka nan wasu mahara sun shiga gidan Rijistaran IKCOE, sun sace shi da matarsa amma yan sanda sun ceto ɗaya

Katsina - Dakarun rundunar 'yan sanda reshen jihar Katsina, ranar Asabar da daddare, sun kuɓutar da ɗan takarar majalisar jiha mai wakiltar Kankiya a inuwar PDP, Ibrahim Tafashiya, daga hannun 'yan ta'adda.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa tun da farko a wannan daren, 'yan ta'addan suka yi garkuwa da Tafashiya a yankin ƙaramar hukumar Kankiya.

Hukumar yan sanda.
'Yan Sanda Sun Yi Gumurzu da Yan Bindiga, Sun Ceto Dan Takarar PDP a Katsina Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Bayan sanar da 'yan sanda lamarin garkuwan, nan take DPO na caji Ofis ɗin Kankiya, SP Iliyasu Ibrahim da 'yan tawagarsa suka toshe hanyar fitar maharan, suka yi gumurzu da su har suka samu nasarar ceto ɗan takaran.

Kara karanta wannan

Katsina: 'Yan Bindiga Sace Mata Masu Juna 2, da Mutum 13 a Sabon Hari

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da wannan nasara a ranar Lahadi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Eh, dagaske ne jami'an mu sun kubutar da Tafashiya daga hannun 'yan ta'adda kuma tuni aka maida shi cikin iyalansa," inji shi.

Yan ta'adda sun shiga gidan Rijistaran IKCOE

Wasu rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'adda sun shiga gidan Rijistaran kwalejin ilimi ta tuna wa da Isah Kaita (IKCOE), Salisu Gide, dake cikin garin Kankiya, inda suka sace shi da matarsa.

Dakarun 'yan sandan sun yi nasarar ceto Giɗe, yayin da suke cigaba da kokarin ceto matarsa da sauran mutanen da maharan suka tattara a harin.

Kakakin 'yan sanda ya ƙara da bayanin cewa an ga 'yan ta'adda a wani wuri dake yankin ƙaramar hukumar Batsari, cikin jihar Katsina.

A wani labarin kuma Wani Rahoto Ya Bankado Yawan Bindigun Dake Hannun Farar Hula ba bisa doka ba a Najeriya

Kara karanta wannan

Da Dumi: Dakarun Sojin Sama Sun Hallaka Yan Ta'addan Boko Haram 49

Wani Rahoto da aka bayyana ya nuna cewa akwai bindigu sama da miliyan Shida a hannun 'yan Najeriya.

Wannan na zuwa ne duk da namijin kokarin da gwamnati tace tana yi na dakile yaɗuwar makamai ba bisa ƙa'ida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel