Katsina: 'Yan Bindiga Sace Mata Masu Juna 2, da Mutum 13 a Sabon Hari

Katsina: 'Yan Bindiga Sace Mata Masu Juna 2, da Mutum 13 a Sabon Hari

  • Miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki Dutsen Reme dake karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina
  • Kamar yadda mazauna yankin suka bayyana, an kwashe wani dalibi tare da wasu mutane uku a yanki daya
  • Duk a Bakorin, miyagun sun sace mata masu juna biyu su biyu tare da 'ya'yansu amma sun sako daya a wurin Kafur

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bakori, Katsina - 'Yan bindiga sun kutsa yankin Low Cost dake Dutsen Reme a karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina inda suka sace mutum hudu.

Wannan lamarin na zuwa ne kamar yadda mazauna yankin suka ce wurin karfe 10 na dare Juma'a, Daily Trust ta rahoto.

Katsina Kidnappers
Katsina: 'Yan Bindiga Sace Mata Masu Juna 2, da Mutum 13 a Sabon Hari. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda wani Ahmed Ridwan, mazaunin Dutsen Reme ta bayyana, maharan sun yi amfani da ruwan saman da ake yi inda suka ci karensu babu babbaka.

“A waya mazauna kauyukan wuraren Maska suka sanar mana cewa 'yan bindiga masu yawa suna kan hanyar zuwa kwatas dinmu kuma da gaggawa muka sanar da 'yan sanda da sojoji. Amma kafin su iso, 'yan bindigan sun sace mutane hudu," Ridwan yace.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Malam Lawal Hamisu Maska, wanda baya nan lokacin da 'yan bindiga suka shiga gidansa, yace abokin hayarsa, Bishir Shitu Sallau, wani ma'aikacin babbar kotu a Funtua yana daga cikin wadanda aka sace tare da Safiyanu, wani dalibin kwalejin ilimi ta Abuja.

Yace:

"Bana gida lokacin da 'yan bindiga suka zo tare da bude kofa. Bishir da Safiyanu sun boye matansu a bandaki, toh lokacin da 'yan bindiga suka balle kofa, sun tambaya mata amma basu gansu ba. A don suka kwashe mazan."

Sakamakon lamarin, Hamisu Maska yace zai kwashe kayansa ya bar gidan da yankin har abada.

“Ni likita ne kuma aikina ne ya kawo min Funtua daga Maska. Wannan tsananin rashin tsaron yasa bani da wani zabin da ya wuce in koma kauyenmu," yace.

A Project Kwatas, sun sace wata Lauratu Jibril da diyar mijinta bayan mijinta Malam Jibril ya sha da kyar.

A wani lamari na daban, 'yan bindiga sama da 20 sun kai hari kauyen Kabomo dake Bakori inda suka sace mutum shida har da mata masu juna biyu.

Salima Lawal, matar daya daga cikin wadanda lamarin ya ritsa da su, yace 'yan bindiga sun kai farmaki wurin karfe 12:15 na daren Talata kuma suka yi garkuwa da mutane shida a gidaje uku.

"Kishiyata tana da ciki wata tara kuma an saceta da 'danta, amma daga baya sun sakota a wurin Huguma dake karamar hukumar Kafur wurin karfe 3 na safe bayan tafiyar kilomita masu yawa, An sacesu da wani Alhaji Sa'adu Gulafa tare da wata mata mai juna tare da 'ya'yanta."

Lawal ya kara da cewa, mijinsu ya tafi Legas neman na abinci yayin da lamarin ya faru.

A yayin da aka nemi jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, yayi alkawarin tuntubar DPO yankin sannan a ji daga bakinsa.

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallacin Juma'a a Zamfara, Sun Kwashe Jama'a

A labari na daban, 'yan bindiga a ranar Juma'a sun sace masallata masu tarin yawa daga Masallacin Juma'a na yankin Zugu dake karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun ce 'yan bindigan sun boye bidigoginsu a cikin kayansu kuma suka shiga masallacin yayin da liman yake dab da fara huduba, Daily Trust ta rahoto.

Maharan sun sanar da wadanda ke wajen Masallacin da su shiga ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel