Da Dumi: Dakarun Sojin Sama Sun Hallaka Yan Ta'addan Boko Haram 49

Da Dumi: Dakarun Sojin Sama Sun Hallaka Yan Ta'addan Boko Haram 49

  • Dakarun Sojojin Najeriya sun yiwa yan ta'addan Boko Haram yayyafin bama-bamai a dajin Sambisa
  • Majiyoyi sun bayyana cewa kimanin yan ta'addan guda hamsin suka hallaka a wannan harin
  • Gwamnatin Najeriya na cigaba da samun nasara kan yan ta'adda masu tada kayar baya a Arewa maso gabas

Jirgin Yakin Super Tucano yayi ruwan wuta kan akalla yan ta'addan kungiyar Boko Haram 49 a harin da Sojoji suka kai sansaninsu uku dake Dajin Sambisa, jihar Borno.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa dakarun Sojin saman rundunar Operation Hadin Kai sun kai hare-haren ne ranar Talata 30 da Laraba 31, ga watan Agusta 2022.

Sojin sun yiwa yan ta'addan yayyafin bama-bamai a Gargash, Minna da Gazuwa, karamar hukumar Bama ta jihar.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mai Magana da Yawun Rundunar 'Yan Sanda a Najeriya Ya Mutu

Tucano
Da Dumi: Dakarun Sojin Sama Sun Hallaka Yan Ta'addan Boko Haram 49
Asali: Twitter

A cewar rahoton Zagazola Makama, shahrarren masanin harkar tsaro a yankin tafkin Chadi, Sojojin sun hallaka dukkan yan ta'addan dake Gargashi a harin ranar 30 ga Agusta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wata majiya daga gidan Soja ta bayyana cewa:

"A ranar 31 ga Agusta, mun sake kai hari Gazuwa bayan bayanai sun nuna cewa yan ta'addan na harkalla a wajen."
"Saboda haka ATF ta tura jiragen yaki wajen inda aka kashe yan ta'addan kuma aka lalata dukiyoyinsu."

Majiyar ta kara da cewa an kashe yan ta'adda 29 a Gazuwa, 4 a Gargashi sannan aka babbaka wasu 16 a Minna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel