Yan Sanda Sun Kama Shaharren Mawakin Najeriya Ice Prince Zamani

Yan Sanda Sun Kama Shaharren Mawakin Najeriya Ice Prince Zamani

  • Jami'an yan sandan Najeriya sun kama fitaccen mawakin gambara na Najeriya Ice Prince Zamani
  • An kama mawakin ne bayan wai ya sace dan sanda wanda ya kama shi saboda tuki babu lamba ya kuma yi barazanar jefa shi a rafi
  • Kakakin rundunar yan sandan Jihar Legas SP Benjamin Hundeyin ne ya wallafa labarin ya kara da cewa za a gurfanar da shi a yau

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Legas - Yan sanda sun kama shahararren mawakin Najeriya wanda aka fi sani da Ice Prince a Legas saboda dukan jami'in dan sanda.

Rahotanni sun ce misalin karfe 3 na daren ranar Juma'a ne yan sandan suka tare mawakin saboda yana tuki ba tare da lamba ba.

Ice Prince
Yan Sanda Sun Kama Fitaccen Mawakin Najeriya Ice Prince Zamani. Hoto: @Benhundeyin @Iceprincezamani.
Asali: UGC

Ice Prince wanda da farko ya yarda zai bi jami'in dan sandan su tafi caji ofis nan take, ya sace dan sandan a cikin motarsa, ya masa duka, kuma ya yi barazanar zai jefa shi cikin kududufi.

Kara karanta wannan

Tsohon Jigon Jam’iyya Ya Fadawa Peter Obi Sirri 5 Na Lashe Zaben Shugaban Kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun yan sandan Jihar Legas SP Benjamin Hundeyin, a shafinsa na Twitter ya ce an kama Ice Prince kuma za a gurfanar da shi a kotu yau.

A cewar Hundeyin:

"Misalin karfe 3 na dare ne aka tsayar da @Iceprincezamani saboda tuki ba bu lasisi. Ya yarda a tafi da shi caji ofis.
"Daga baya, ya sace dan sandan da ke cikin motarsa, ya masa duka, kuma ya yi barazanar zai jefa shi cikin rafi.
"An kama shi kuma za a gurfanar da shi a yau."

Martanin wasu yan Najeriya

Labarin kama Ice Prince ya bazu cikin kankanin lokaci kuma mutane sun fara tofa albarkacin bakinsu.

Kinghashthattag:

"Kana tunanin babu dokoki a Najeriya har sai ..."

Kika_falz:

"Shi ya nemi rikici."

Mz_barbss:

"Ka ya ... Ya yi kuskure.."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An Ceto Mutum 3 Daga Ginin Da Ya Rufta A Kasuwar Kano, Akwai Saura Da Aka Kasa Fito Da Su

Poshestmag:

"Ban yarda da yan sandan Najeriya ba, bari mu ji bangarensa tukunna."

Olayemimclean_:

"Lallai yana da karfin hali. Hmmmm! Ya yi bye bye da yancinsa."

Kennedyexcel:

"Bari mu ji daga gare shi saboda kuna karya sosai.."

Rundunar Yan Sandan Najeriya Ta Umurci Mawaki Portable Ya Kai Kansa Ofishinta Ko Ta Kamo Shi

A wani rahoton, Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Ogun ta umurci fitaccen mawakin Najeriya, Habeeb Okikiola da aka fi sani da Portable ya kai kansa ofishinsu mafi kusa nan take ko kuma a kama shi.

Hakan ya biyo bayan zargin duka da aka ce ya yi wa tsohon DJ dinsa mai suna DJ Chicken, rahoton Daily Trust.

A wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, Portable, wanda ya yi magana da harshen Yarbanci ya umurci yaransa su yi wa DJ Chicken duka kan zargin ya tura wa matarsa sako.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164