An Ceto Mutum 3 Daga Ginin Da Ya Rufta A Kasuwar Kano, Akwai Saura Da Aka Kasa Fito Da Su

An Ceto Mutum 3 Daga Ginin Da Ya Rufta A Kasuwar Kano, Akwai Saura Da Aka Kasa Fito Da Su

  • Wani gini mai bene biyu a kasuwar Kano ya rufta ya danne ma'aikata da yara masu talla da mai siyar da abinci a Beirut road da ke birnin Kanp
  • Jami'an tsaro masu bada dauki da suka kunshi yan sanda, jami'an kwana-kwana, ma'aikatan SEMA da jami'an FRSC sun isa wurin don taimako
  • Ma'aikatan sun yi nasarar ceto mutane uku bayan sun haka rami sun ciro su amma har yanzu akwai sauran mutane da ake jin muryansu amma ba a gano inda suke ba

Jihar Kano - Wani gini da ake kan aikinsa ya rushe a daya daga cikin kasuwannin wayoyin salula wato GSM a Kano.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ginin yana Beirut road ne, wani layi da mutane kan yawan hada-hada.

Gini A Kano
Jihar Kano: Gini Ya Rushe, Ya Danne Mutane Da Dama A Kasuwa. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Babban Magana: Masallatai Da Coci-Coci Suna Satar Ɗanyen Man Fetur A Najeriya, In Ji Shugaban NNPC, Kyari

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ana fargabar mutane da dama sun makale a ginin da ya rufta duk da cewa a yanzu ba a tabbatar da adadinsu ba.

Bidiyon ginin da ya rushe

TVC News ta wallafa bidiyon ginin mai bene biyu da ya rushe a kasuwar ta Kano inda aka gano dandazon mutane sun taru a wurin da abin ya faru.

An ji muryar wani daga cikin mutanen yana cewa 'a kawo mana agaji'.

Shaidan gani da ido ya magantu

Wani wanda abin ya faru a idonsa ya ce wasu mutane na cikin ginin a lokacin da ya rushe kuma ba a iya ceto su ba saboda babu kayan aiki.

An ji muryar daya daga cikinsu a lokacin da aka kira shi a wayar tarho.

Daya cikin shaidun na ido ya ce:

"Yanzu muka kira lambarsa kuma yana daga wayan. Kawai dai babu hanyar da zai iya fitowa ne."

Kara karanta wannan

Daga Karshe: Wata Kabila A Duniya Ta Shafe, Mutum 1 Da Ya Rage Ya Koma Ga Allah

Masu kai dauki sun isa wurin, an ceto mutum biyu

Daya cikin tawagar masu ceto da suka isa wurin da wuri ya ce, motar hakar rami tana hanyar zuwa wurin domin taimakawa wurin ceto wadanda suke makale cikin ginin.

Bayan kankanin lokaci, an ceto mutane biyu daga ginin, hakan ya kawo adadin wadanda aka ceto zuwa uku. An garzaya da dukkansu asibiti.

Daya daga cikin wadanda suka kawo daukin ya ce akwai sauran mutane da dama a har da mata da yara da ginin ya danne.

Ya ce:

"Wasu yara da ke sayar da kwai, mace mai sayar da abinci duk suna ciki. Mun haka rami mun ciro mutum uku. Sauran suna ciki, muna iya jin sautinsu amma ba mu gano inda suke ba."

Mun musu gargadi amma suka ce babu abin da zai faru

Ya kara da cewa tunda farko sun taba lura ginin yana tsagewa suka janyo hankulan ma'aikatan amma suke ce musu babu abin da zai faru.

Kara karanta wannan

Washegarin Biki, Ango da 'Yan Biki 5 Sun Sheka Lahira, Wasu Suna Asibiti Rai a Hannun Allah

Ya kara da cewa:

"Kayan aikin da za su kawo ba zai yi komai ba. Mun gargade su (maginan) tuntuni kuma wannan shine karo na biyu amma ba su yi komai ba."

Cikin masu aikin ceton akwai jami'an Kwana-Kwana, FRSC, Yan sanda da Ma'aikatan SEMA.

Legit Hausa ta samu tattaunawa da wani da ke sayar da kayan wayoyin salula a layin na Beirut mai suna Usman wanda ya yi karin haske kan lamarin.

Ya ce abin da ya faru kaddara daga Allah (SWT) amma akwai sakaci daga bangaren masu aikin ginin domin kowa na ganin wasu sassan ginin na tsagewa amma suka nuna ba abin damuwa bane,

Ya kuma ce yana fatan hukumomin da nauyin kula da irin wannan gine-ginen ya rataya a kansu za su rika saka idanu sosai domin tabbatar da cewa ana bin dokokin gini don kaucewa faruwar hakan a gaba.

Kalamansa:

"Gaskiya a gani na akwai laifin ma'aikatan da ke ginin domin suna ganin alamun tsagewa amma ba su dakata ko daukan matakin da ya dace ba har sai da lamari ya yi muni."

Kara karanta wannan

Karfin hali: An kama wani sojan bogi da ke yiwa mata fashi da makami

Ganduje Ya Soke Lasisin Filin da Bene Ya Kashe Mutane a Kano

A wani cigaba da aka samu, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ƙwace filin wurin da Bene mai hawa uku ya rushe a Beirut Road, kasuwar waya dake cikin birnin Kano.

Dailytrust ta ruwaito cewa Ginin wanda ya ruguje sanar Talata, ya yi sanadin mutuwar mutum biyu yayin da wasu Bakwai ke kwance suna jinya.

Duk da cewa har yanzun ba'a tantance asalin masu wurin ba, amma shugaban hukumar ba da agajin gaggawa (SEMA), ya ce ginin ba'a yi shi yadda ya kamata ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel