Tsohon Jigon Jam’iyya Ya Fadawa Peter Obi Sirri 5 Na Lashe Zaben Shugaban Kasa

Tsohon Jigon Jam’iyya Ya Fadawa Peter Obi Sirri 5 Na Lashe Zaben Shugaban Kasa

  • Dr. Kayode Ajulo, ya bayyana cewa ba a iya lashe zabe daga samun shahara a shafukan sada zumunta kadai
  • Tsohon sakataren jam’iyyar LP ta kasa, ya fadawa Peter Obi ya nemi nasara a jihohi shida baya ga Anambra
  • Kayode Ajulo yana so Obi ya hada-kai da manyan kasa, wasu Gwamnoni a PDP da kuma kungiyoyin kwadago

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Daily Trust ta rahoto Dr. Kayode Ajulo yana cewa idan har ba ayi amfani da dandalin sadarwan wajen fitowa zabe ba, ya zama an yi aikin banza.

Dr. Kayode Ajulo ya fadakar da Peter Obi mai neman zama shugaban kasa a karkashin inuwar LP cewa sai ya tashi tsaye kafin ya lashe zaben 2023.

Wannan Lauya wanda ya kware wajen sanin kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi wannan bayani ne a wani jawabi da ya fitar a ranar Laraba da ta wuce.

Kara karanta wannan

Abokin Takarar Atiku Ya Fara Tsorata, Ya Gagara Hakura da Maganar Peter Obi

“Kafofin sada zumunta suna da amfani wajen nuna shahara, amma babu tabbacin za su samawa mutum kuri’u a zabe.
Abin da za iyi tasiri wajen fito da sabon shugaban kasa shi ne kuri’un gaskiya da aka kada a rumfunan zaben da ke kasar nan.”

- Dr. Kayode Ajulo

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Inda kuri’u suke a zaben Najeriya

"Akwai rumfunan zabe 176, 000 a Najeriya da kuma adadin mutane miliyan 96 da suka yi rajistar kada kuri’arsu a zabe.
Kusan 93, 000 na rumfunan nan suna Arewacin Najeriya, yayin da ake da rumfuna 80, 000 a yankin kudancin Najeriya.
Peter Obi
Peter Obi da wasu jagororin LP Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter
Arewa maso yamma ta fi kowa yawan rumfunan zabe, akwai 41, 671 da kuma mutane miliyan 22.67 masu rajistar zabe.
Daga nan sai yankin Kudu maso yammacin Najeriya a bayansu da rumfuna 34,808 da rajistar mutane miliyan 18.3

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: ‘Yan Gari Sun yi Wa Shugaban Karamar Hukumarsu Ruwan Dutse

Arewa ta tsakiya na da rumfuna 27, 514 da rajistar mutum miliyan 15.68. Kudu maso kudu na da rumfuna 27, 126 da mutum miliyan 15.3.
Akwai rumfuna 24, 006 da mutum miliyan 12.9 a Arewa ta gabas, a Kudu maso gabas akwai rumfuna 21, 631 da rajistar miliyan 11.49.”

- Dr. Kayode Ajulo

Galaba a Anambra da wasu Jihohi

Rahoton yace Ajulo ya fadawa LP dole sai Obi ya yi nasara a jihohi shida da ke wajen Anambra kafin ya iya samun nasara a kan sauran jam’iyyu.

Haka zalika ya yi kira gare shi ya ziyarci Olusegun Obasanjo, Aliyu Gusau da sauran manya.

Lauyan ya fadawa Obi ya hada-kai da gwamnonin PDP da ke mulki a Ribas, Oyo da Benuwai. Baya ga haka ya yi amfani da kungiyoyin NLC da TUC.

Ci da addini

An samu labari Ifeanyi Arthur Okowa ya zargi ‘Dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar Labor Party watau Peter Obi da kokarin ci da addini.

Kara karanta wannan

‘Dan gwagwarmaya Ya Fadawa Atiku, Obi da Kwankwaso Hanyar Doke Tinubu a Saukake

A manyan ‘yan takaran shugaban kasa da ake da su a zaben 2023, Peter Obi ne kurum kirista, don haka yake samun damar zama da kiristoci a coci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel