Rundunar Yan Sandan Najeriya Ta Umurci Mawaki Portable Ya Kai Kansa Ofishinta Ko Ta Kamo Shi

Rundunar Yan Sandan Najeriya Ta Umurci Mawaki Portable Ya Kai Kansa Ofishinta Ko Ta Kamo Shi

  • Rundunar yan sandan Najeriya ta Jihar Ogun ta umurci shahararren mawaki Habeeb Okikiola da ake kira Portable ya kai kansa ofishinsu
  • Hakan ya biyo bayan wani bidiyo ne da ke yawa a kafafen sada zumunta inda aka gano Portable yana umurtar 'yaransa' su yi wa tsohon DJ dinsa duka
  • Sanarwar da kakakin yan sandan, Abimbola Oyeyemi ya fitar ta ce idan har mawakin bai kai kansa ba za ta bada umurnin a kamo shi da karfin ikon doka

Jihar Ogun - Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Ogun ta umurci fitaccen mawakin Najeriya, Habeeb Okikiola da aka fi sani da Portable ya kai kansa ofishinsu mafi kusa nan take ko kuma a kama shi.

Kara karanta wannan

Wani Fasto ya fadawa mutane wanda za su zaba tsakanin Tinubu, Atiki da Obi a 2023

Hakan ya biyo bayan zargin duka da aka ce ya yi wa tsohon DJ dinsa mai suna DJ Chicken, rahoton Daily Trust.

Mawaki Portable
Rundunar Yan Sandan Najeriya Ta Umurci Mawaki Portable Ya Kai Kansa Ofishinta Ko Ta Kamo Shi. Hoto: Portable.
Asali: Instagram

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, Portable, wanda ya yi magana da harshen Yarbanci ya umurci yaransa su yi wa DJ Chicken duka kan zargin ya tura wa matarsa sako.

Martanin yan sanda

A wani matakin gaggawa da rundunar yan sandan ta dauka, mai magana da yawunta, Abimbola Oyeyemi, ya umurci wanda ya yi wakar 'zazu' din ya kai kansa ofishin yan sanda mafi kusa a jihar ko a kama shi.

Oyeyemi, cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun a ranar Litinin, ya bayyana abin a matsayin 'dabbanci'.

Sabon salo: Birkitaccen mawaki ya fito takarar gaje Buhari a jam'iyyun siyasa har biyu

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun sako shugaban kauye don ya tara N100m ya karbi mutanensa 30

A wani rahoton, shahararren mawakin Najeriya, Portable ya sa jama'a a shafukan sada zumunta suna ta maganganu bayan da ya yada hoton yakin neman zabensa a Instagram.

Mawakin ya bayyana sha'awarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa amma a jam'iyyar APC da SDP duk dai a lokaci guda.

A taken kamfen din nasa, ya bayyana cewa lokaci ya yi da jama'ar tituna za su mamaye gwamnati yayin da ya bayyana a manufarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel