Mutane Guda 15 Sun Nutse A Rafi A Borno, An Ciro Gawarwaki

Mutane Guda 15 Sun Nutse A Rafi A Borno, An Ciro Gawarwaki

  • Kimanin mutane 15 ne suka riga mu gidan gaskiya a Maiduguri jihar Borno sakamakon nutsewa da suka yi a Rafin Ngadabul
  • Mohammed Usman, shugaban hukumar NEMA na yankin arewa maso gabas ya tabbatar da afkuwar lamarin yayin hira da NAN
  • Usman ya ce NEMA ta tallafawa wadanda abin ya shafa sannan ta tunatar da iyayen yara a dena bari suna zuwa Rafin da ya yi ambaliya domin wanka

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Borno - A kalla gawarwaki guda 15 ne aka ciro daga Rafin Ngadabul da yayi ambaliya a Maiduguri, Jihar Borno, The Punch ta rahoto.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na kasa NEMA na yankin arewa maso gabas, Mohammed Usman ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Laraba yayin hira da NAN a Maiduguri.

Gwamnan Borno
Mutane Guda 15 Sun Nutse A Rafi A Borno, An Ciro Gawarwaki. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Usman ya ce ana samun karuwar mutane da ke nutsewa a rafin da ya yi ambaliya a garuruwan da ke gabar rafin a Maiduguri.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yadda Na Magance Yajin Aikin ASUU Cikin Kwana Ɗaya, Jonathan Ya Yi Jawabi Mai Ratsa Jiki

Ya yi kira ga iyaye da masu kula da yara su rika yi wa yaransu gargadi su dena zuwa wanka a rafin don gudun nutsewa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Usman ya ce:

"NEMA a matsayinta na hukuma mai kiyayye afkuwar iftila'i ta fara aikin wayar da kan mutane da rabon kayan tallafi ga garuruwan da abin ya shafa."

A bangarenta, Rundunar hukumar tsaro ta NSCDC na jihar Borno ta tura jami'anta gaban rafin domin su rika korar yara da ke tururuwan zuwa rafin domin yin wanka.

Jirgin ruwa maƙare da mutane yan yawon sallah ya Nutse a Katsina, Rayuka sun salwanta

A wani rahoto, kun ji cewa a ƙalla gawarwaki 18 aka tsamo yayin da aka ayyana ɓatan wasu mutane shida yayin da wani jirgin ruwa ya kife a yankin ƙaramar hukumar Mai'adua a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: ‘Yan Gari Sun yi Wa Shugaban Karamar Hukumarsu Ruwan Dutse

Wani da ke zaune a garin mai suna Lawal Sakatare, wanda ta tabbatar da faruwar lamarin ga Daily Trust, ya ce mutum 24 da ke shagalin sallah ne suke cikin kwalekwalen kafin ya kife.

Ya ce guda 18 daga cikin su mafi yawanci ƙananan yara suka nutse kuma Allah ya musu rasuwa sanadiyyar hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel