Yadda Na Magance Yajin Aikin ASUU Cikin Kwana Daya, Jonathan Ya Yi Jawabi Mai Ratsa Jiki

Yadda Na Magance Yajin Aikin ASUU Cikin Kwana Daya, Jonathan Ya Yi Jawabi Mai Ratsa Jiki

  • Dakta Goodluck Ebele Jonathan, tsohon shugaban kasar Najeriya ya yi magana game da yajin aikin malaman jami'o'i ASUU da aka shafe a kalla wata shida ana yi
  • Tsohon shugaban kasar ya bada labarin yadda a zamaninsa ASUU ta tafi yajin aiki na wata hudu har sai da ya kira taro da kansa suka kashe dare aka janye yajin aikin
  • Jonathan ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba 31 ga watan Agusta a birnin tarayya Abuja wurin bikin murnar cikar Bishop Kukah shekara 70 a duniya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana yadda gwamnatinsa a cikin kwana daya ta magance yajin aikin wata hudu da kungiyar malaman jami'o'i ASUU ta taba yi.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba wurin bikin cikar Bishop Mathew Kukah shekaru 70 da haihuwa da aka yi a Cibiyar Kukah da ke Abuja, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Hotunan Jana'izar Mutune 7 Yan Gida Ɗaya Da Suka Rasu Bayan Sunyi Karin Kumallo Da Dambu A Sokoto

Jonathan
Jonathan: A Cikin Kwana Daya Na Warware Matsalar Yajin Aikin ASUU. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit Hausa ta rahoto cewa jami'o'i a Najeriya sun fara yajin aiki tun watan Fabrairu kan rashin cika musu bukatunsu da gwamnatin tarayya ba ta yi ba.

Jonathan ya bada labarin yadda ya hana kansa barci sai da aka warware matsalar ASUU

Jonathan ya ce:

"Tafiyar da kasar da muke ciki abu ne mai sarkakiya, yanzu muna maganan yajin aikin ASUU, nima lokaci na, ASUU ta yi yajin aiki na wata hudu, kwamiti daban-daban suna ta taro amma abin bai warware ba. Na ce ta yaya yaranmu za su zauna a gida na wata hudu? Sai na kira taron dukkan shugabannin ASUU.
"Ni na jagoranci taron tare da mataimaki na, Antoni Janar yana wurin, na ce dole mu warware matsalar a cikin daren nan. Sakataren Gwamnatin Tarayya yana wurin, ministocin ilimi suna wurin, ministocin kudi da kwadago suma suna wurin, dole kowa ya yi.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Wani abu zai faru, gwamnati ya share ASUU, ta kira ganawa da shugabannin jami'o'i

"Kuma ina ganin kasancewa ta a wurin ya taimaka mana kammala abin da wuri. Amma fa sai karfe 5.30 na asubahi muka kammala kuma aka janye yajin aiki, don haka akwai batutuwa."

Jonathan ya ce Bishop Kukah, duk da abokanta da ya ke yi da shugabanni yana sukarsu idan yana ganin ba su yi wasu abubuwan dai-dai ba, har da shi kansa.

Yajin Aiki: An Huro Wa Shugaban ASUU Wuta Akan Kiran Wasu Jami'o'in Najeriya "Jabu"

A wani rahoton, Farfesa Emmanuel Osodoke, shugaban kungiyar malaman jami'o'in Najeriya, ASUU, ya kira wasu jami'o'in jihohin Najeriya a matsayin makarantun 'bogi', The Cable ta rahoto.

Furta wannan kalmar ya janyo masa suka da daga wasu jami'o'in jihohin da kuma yan Najeriya a dandalin sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel