Jirgin ruwa maƙare da mutane yan yawon sallah ya Nutse a Katsina, Rayuka sun salwanta

Jirgin ruwa maƙare da mutane yan yawon sallah ya Nutse a Katsina, Rayuka sun salwanta

  • Aƙalla mutum 18 aka zaro duk a mace mafi yawa kananan yara bayan wani Kwalekwale ya yi hatsari a Katsina
  • Wani shaida ya bayyana cewa Jirgin ya ɗakko mutum 24, har yanzun ana neman ragowar mutum 6 a raye ko a mace
  • Lamarin wanda ya rutsa da yan yawon shagalin ƙaramar Sallah ya faru ne a ƙaramar hukumar Mai'adua

Katsina - Zuwa yanzu aƙalla gawarwaki 18 aka tsamo yayin da aka ayyana ɓatan wasu mutum 6 yayin da wani Jirgin ruwa ya kife a yankin ƙaramar hukumar Mai'adua a jihar Katsina.

Wani mazauni, Lawal Sakatare, wanda ta tabbatar da faruwar lamarin ga Daily Trust, ya ce mutum 24 da ke shagalin sallah ne ke cikin Kwalekwalen kafin ya kife.

Taswirar jahar Katsina.
Jirgin ruwa maƙare da mutane yan yawon sallah ya Nutse a Katsina, Rayuka sun salwanta Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce 18 daga cikin su mafi yawanci ƙananan yara suka nutse kuma Allah ya musu rasuwa sanadiyyar haka.

Lawal Sakatare ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"14 daga ciki sun fito ne daga ƙauyen Tsabu yayin da mutum.4 yan kauyen Dogo Hawa ne. Haka nan gawarwaki 15 daga cikin 18 an binne su a garin Mai'adua yau Alhamis, har yanzun ba'a gano sauran mutum shida da suke tare ba."

Ya ƙara da cewa tawagar mutane daga dukkan ƙauyukan na cigaba da aikin ceto, suna kokarin gano ragowar mutum shida duk da cewa an cire rai da tsamo su a raye.

Da aka tuntubi kakakin hukumar yan sanda reshen Katsina, SP Gambo Isah, bai amsa kiran ba kuma bai turo amsar saƙonnin da aka tura masa ba kan lamarin.

Kwastam sun kashe mutum ɗaya a Jibia

Sai dai a wani cigaban kuma, Motar Kwastam da ta biyo yan Fasakwauri ta halaka wani mutum ɗaya har Lahira a Jibia ranar Laraba.

Rahoto ya nuna cewa wasu mutum uku sun jikkata kuma bayanai sun nuna mamacin na kan hanyarsa ne ta zuwa Katsina daga Jibia.

Kwanturolan kwastam na Katsina, Comptroller Dalha Wada Chedi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce yanzu haka suna kan bincike.

Legit.ng Hausa ta tattauna da wani mazaunin garin Mai'adua wanda ya shaida faruwar lamarin, ya ce mutum 15 ne suka rasa rayuwarsu.

Mutumin mai suna Abubakar Sadeeq Mai'adua ya shaida wa wakilin mu cewa:

"Mutanen dake cikin jirgin za su kusa 30, kuma tsautsayi ne ya afka musu ka san yanayin jirgin ruwa irin na mu. Wasu sun tsira wasu kuma na kwance a Asibiti."
"Mutane na cigaba da aikin ceto domin ana tsammanin da sauran wasu a cikin ruwan, mafi yawan su dai yara ne da ke yawon Sallah."
"Mutum 1y ne suka mutu kuma tuni aka gudanar da Jana'izar su anan garin Mai'adua."

A wani labarin na daban kuma Miji ya lakaɗa wa matarsa dukan tsiya, ya yi barazanar kasheta kan yawan kwalliya 'Make-Up'

Yan sanda a Legas sun gurfanar da wani Magidanci gaban Kotu kan zargin barazanar kashe matarsa.

Ana tuhumar Magidancin da lakaɗawa matarsa dukan tsiya da kuma faɗa mata zai ga bayanta kan yawan amfani da Make-Up.

Asali: Legit.ng

Online view pixel