Tattalin arziki: Mataimakin Shugaban kasa, Osinbajo ya yi wa Gwamnan CBN kaca-kaca

Tattalin arziki: Mataimakin Shugaban kasa, Osinbajo ya yi wa Gwamnan CBN kaca-kaca

  • Mataimakin shugaban kasa ya yi jawabi a wajen bitan da aka shiryawa Ministoci
  • Farfesa Yemi Osinbajo ya yi tir da tsare-tsaren bankin CBN, yace akwai gyara
  • Osinbajo ya bayyana wasu abubuwa da suke kara jawo matsalar tattalin arziki

Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya soki tsarin da babban bankin Najeriya na CBN ya dauka a kan batun canjin kudin kasashen waje.

Premium Times tace Yemi Osinbajo ya ba babban bankin kasar shawara ya sake tunani kan batun canji.

Da yake magana a wajen taron bitar da aka shirya wa Ministoci a ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba, 2021, Farfesa Osinbajo ya kawo wannan batun.

A cewar Farfesa Yemi Osinbajo, farashin Naira ya yi kasa sosai a kasuwar canji, wanda a cewarsa hakan ba shi ne asalin zahirin abin da yake kasuwan ba.

Kara karanta wannan

Tunde Bakare ya yi magana game da shirin takarar 2023 bayan ya sa labule da Buhari

Akwai matsala a game da farashin canji

“A game da farashin kudin canji, ina tunani ya kamata mu matsa da farashin mu ta yadda zai yi daidai da kasuwa, yadda ya kamata.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wannan shi ne ra’ayi na, ta haka ne za a kara yawan shigowar kudi a kasuwa.” – Osinbajo.

Buhari, Mataimakin Shugaban kasa
Shugaba Buhari da Mataimakinsa, Farfesa Osinbajo Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mataimakin shugaban kasa ya dura kan CBN

Farfesa yace ba zai yiwu a rika samun Dala a irin wannan yanayi ba. Sahara Reporters tace Osinbajo ya soki dabarun shawo kan annobar cutar COVID-19.

Osinbajo yana ganin daga cikin abubuwan da ke kawo matsalar tattali shi ne kamfanoni ba su samun kudin kasar wajen da za su sayo kayan da ake bukata.

A jawabinsa, Osinbajo yace akwai bukatar CBN da sauran ma’aikatu da hukumomin gwamnati su rika tafiya a shafi guda, yace a yanzu a kan samu kwamcala.

Kara karanta wannan

Mun rabawa matasan Najeriya 7,057 tallafin N3bn ta shirin NYIF, CBN

“Kowa ya san ajiyar da ke cikin asusun mu zai iya karu wa. Nayi imani cewa akwai gyara a tsarin da bankin CBN ya dauka, wannan ra’ayi na kenan.”
“Alal hakika duk wadannan wasu abubuwa ne da gwamnan CBN ya kamata ya samu lokaci, ya shawo kansu. Zai iya shawo kan su gaba daya.” - Osinbajo

Babu maganar wahalar fetur

Shugabannin NUPENG sun dauki mataki a kan yajin-aikin da suka yi niyyar shiga saboda munin hanyoyi da wasu sabani tsakaninsu da gwamnatin Najeriya.

Shugaban kungiyar NUPENG na reshen Kudu maso yamma, Tayo Aboyeji ya shaida wa hukumar dillacin labarai na kasa, NAN, cewa sun fasa yin yajin-aikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel