Sanusi, Deji Na Akure, Da Wasu Sarakuna 8 da Aka Tsige a Tarihin Najeriya

Sanusi, Deji Na Akure, Da Wasu Sarakuna 8 da Aka Tsige a Tarihin Najeriya

 • Sarakunan gargajiya akalla 10 ne aka raba da kujerunsu na sarauta saboda wata matsala da suka samu tun bayan farkon jamhuriya ta hudu ta Najeriya
 • Wadannan sarakuna dai sun rasa rauwunansu ne saboda wasu munanan ayyukansu da suka hada da shafawa ido shuni, rikon sakainar kashi, cin zarafin mata da kwankwadar kayan shaye-shaye
 • Kadan daga cikinsu, kuma shahararru sun hada da tsigaggen Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi II da Adesina Osupa, Deji na Akure na jihar Ondo

Najeriya - Tsarin masarautun gargajiya a Najeriya ka tafiya ne a karkashin kananan hukumomi kuma gwamnonin jihohi, kuma su ke da karfin ikon nadi ko da tsige sarakunan gargajiya a jihohinsu.

Tun bayan kafa jamhuriya ta hudu a Najeriya, akalla sarakuna 10 ne suka rasa rauwnansu a fadin kasar nan, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Jerin wasu sarakuna 10 da aka raba rauwunansu a tarihin Najeriya
Sanusi, Deji na Akure, da wasu sarakuna 8 da aka tsige a Najeriya | Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, @PremiumTimesng
Asali: Twitter

Na baya-bayan nan da ya jawo cece-kuce dai shi ne na Kano, lokacin da gwamna Ganduje na jihar ya tsige Muhammadu Sanusi II kuma sarkin Kano na 14.

A 2019 ne gwamna Ganduje ya fusata wasu Kanawa yayin da ya tsige sarkinsu dan boko kuma dan kwalisa, wanda tsohon gwamna ne na babban bankin kasa (CBN).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A daya bangaren, Deji na Akure, Oba Oluwadamilare Adesina Osupa III ya rasa kujerarsa saboda amfani da kujerarsa wajen aikata abubuwan da suka saba al'ada.

An ruwaito cewa, wannan basaraken gargajiya ya bugi matarsa, lamarin da ya jawo cece-kuce har aka tsige shi.

Jerin wasu sarakunan da aka tsige

 1. Sanusi Lamido Sanusi II - Sarkin Kano
 2. Oluwadamilare Adesina Osupa - Deji na Akure a jihar Ondo
 3. Abubakar Atiku - Sarkin Zuma a Zamfara
 4. Hussaina Umar - Sarkin Dansadau a Zamfara
 5. Sulaiman Ibrahim - Hakimin Birnin Tsaba a Zamfara
 6. Mustapha Jokolo - Sarkin Gwandu a Kebbi
 7. Cif Monday Frank Noryea - Sarkin gargajiya na masarautar Baabe a jihar Ribas
 8. Eze Joseph Okor - Ivi na Akaeze a jihar Ebonyi
 9. Eze Michael Orji a jihar Ebonyi
 10. Aslem Aidenojie - Onojie na Masarautar Uromi a jihar Edo (Adams Oshiomhole ne ya tsige shi bisa cin zarafin mata, amma daga baya Gwamna Godwin Obaseki ya sake mai da masa rawaninsa)

Kada Ku Kuskura Ku Zabi Shugabannin da Ba Su Cancanta Ba, Shawarin Sarki Sanusi Ga ’Yan Najeriya

A wani labarin, Sarkin Kano na 14, kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya ba 'yan Najeriya shawarin irin shugabannin da ya kamata su zaba a zaben 2023 mai zuwa.

Muhammadu Sanu II, ya ce ya kamata 'yan Najeriya natsu su zabi shugabannin da ke da kwarewa ta gudanar da kasa a zabe mai zuwa, kuma su kauda batun kabilanci, TheCable ta ruwaito.

Sanusi ya bayyana hakan ne a jiya Laraba 24 ga watan Agusta a jihar Legas taron The August Event 2022 da gidauniyar Moses Adekoyejo Majekodunmi tare da hadin gwiwar Asibitocin Santa Nicholas suka shirya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel