Duk da kokarin Hisbah na hana shan barasa, 'yan Najeriya sun kwankwadi ta N600bn a wata shida

Duk da kokarin Hisbah na hana shan barasa, 'yan Najeriya sun kwankwadi ta N600bn a wata shida

  • Rahoto ya fito ya bayyana adadin kudaden da 'yan Najeriya suka kashe wajen kwankwadar barasa a bana
  • Kamfanin Champion ne a kan gaba wajen kwasar riba mai gwabi a fannin barasa, ya samu kaso mai tsoka na karuwa
  • Hukuma a jihohin Arewacin Najeriya na yaki da shan barasa da dillacinta, lamarin da ke tunzura wasu jama'ar kasar

Najeriya - Wani rahoton da kafar yada labarai ta BBC ta fitar ya ce, akalla barasar N599.11 ne 'yan Najeriya suka kwankwada a cikin watanni shida kacal na farkon 2022.

Rahoton ya fito ne daga kamfanonin barasa hudu na Najeriya, kuma ya mai da hankali ne daga watan Janairun bana zuwa watan Yunin da ta gabata.

Guinness da Champion na daga cikin kamfanonin hudu, kuma sun ce kwalliya ta biya kudin sabulu, domin kuwa kamfanonin barasa a Najeriya sun samu riba mai tsoka a wannan shekarar.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Sanusi da wasu sarakuna 9 da aka taba tsige su a kujerunsu a tarihin Najeriya

Adadin kudaden 'yan Najeriya suka kashe a kwankwadar barasa cikin wata shida
Duk da kokarin Hisbah na hana shan barasa, 'yan Najeriya sun kwankwadi ta N600bn a wata shida | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

A cewarsu, sun samu karin 31.2% cikin 100% na zunzurutun riba, idan aka kwatanta da N456.44bn da suka yi ciniki a shekarar da ta gabata; 2021.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahoton ya kuma ce, a fili yake yadda 'yan Najeriya ke kara adadin barasar da suke kwankwada a wuni idan aka kwatanta da wasu lokuta a baya.

Hukumar Hisbah a Arewacin Najeriya na matsa lamba wajen shigo da barasa da dillacinta a jihohin yankin.

Yadda kamfanonin hudu suka kara rubanya riba a 2022

Da take bayyana adadin kason da kowanne kamfani ya samu na riba a farkon shekarar nan, jaridar Vanguard ta yi bayani dalla-dalla na kason da ya karu kamar haka:

  1. Kamfanin barasa na Champion ya karu da 41.6%
  2. Kamfanin barasa na kasa da kasa (International Breweries) ya karu da 35.9%
  3. Kamfanin barasa na Najeriya (Nigerian Breweries) ya karu da 30.9%
  4. Kamfanin barasa na Guinness ya karu da 28.9%

Kara karanta wannan

2023: Sarkin Kano Sanusi ya ba 'yan Najeriya shawarin shugaban da za su zaba

‘Yan Hisbah sun kama litoci fiye da 2000 na burkutu da kwalaben giya 96 a Jigawa

A wani labarin, rundunar Hisbah na reshen jihar Jigawa ta bayyana cewa ta yi nasarar yin ram da wasu kayan barasa a makon nan.

Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Laraba, 30 ga watan Maris 2022 cewa wannan abin ya faru ne a karamar hukumar Maigatari.

Hukumar ta ce jami’anta sun karbe duro takwas masu cin lita 25 cike da giyar hatsi ta gargajiya wanda aka fi sani da burkutu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel