Aure Yakin Mata: Bidiyon Yadda Diyar Sanata Sahabi Ta Rungume Mahaifinta Cikin Kuka Yayinda Za a Kaita Dakinta

Aure Yakin Mata: Bidiyon Yadda Diyar Sanata Sahabi Ta Rungume Mahaifinta Cikin Kuka Yayinda Za a Kaita Dakinta

  • An kammala shagalin biki daga bangaren amarya Amina Ummi, diyar Sanata Sahabi Ya'u Inda aka sada ta da gidan mijinta
  • A bidiyon da ya yadu a shafukan soshiyal midiya, an gano amaryar rungume da mahaifinta suna kukar rabuwa da junansu yayin da jama'ar wajen suka taya su
  • Amina dai ta amarce da angonta Muhammad Auwal wanda ya kasance Majikiran Adamawa a karshen makon nan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zamfara - Kowasu iyaye burinsu shine aurar da yaransu mata da zaran sun kai munzalin aure don su fara tasu rayuwar da iyalinsu.

Sai dai masu iya magana kan yiwa aure lakabi da yakin mata domin za ta bar iyaye da yan uwa ta koma rayuwa a wani sabon wuri da sabbin dangi.

Diyar Sanata Sahabi
Aure Yakin Mata: Bidiyon Yadda Diyar Sanata Sahabi Ta Rungume Mahaifinta Cikin Kuka Yayinda Za a Kaita Dakinta Hoto: fashionseriesng
Asali: Instagram

Hakan ce ta kasance ga Amarya Amina Ummi, diyar Sanata Sahabi Ya’u mai wakiltan yankin Zamfara ta arewa.

Kara karanta wannan

Kyawawan Hotunan Daurin Auren Wasu Yan Najeriya A Dubai Ya Yadu, Sun Yi Shaglin Bikinsu A Saukake

An dai daura auren Amina da Angonta Muhammad Auwal wanda ya kasance Majikiran Adamawa a ranar Asabar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai Ummi da mahaifinta sun tsuma zukata a shafukan soshiyal midiya bayan bayyanan bidiyonsu na bankwana da juna.

A cikin bidiyon da shafin fashionseriesng ya wallafa a Instagram an gano inda aka yiwa Amina rakiya don tayi bankwana da mahaifinta Sanata Ya’u yayin da za a sada ta da dakin mijinta.

Sai dai kuma da isanta gaban mahaifin nata sai suka rungume juna yayin da take kuka wiwi na kewar rabuwa da mahaifinta. Mutane da dama da ke wajen ma sun tayata zubar da hawaye yayin da suke ta kokarin banbareta daga jikin mahaifin nata.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

ubmeerat_treats ta ce:

"baba."

fatoushclothing ta yi martani:

Kara karanta wannan

Bidiyoyin Shagalin Dinan Kyakkyawar Diyar Sanata Sahabi

"Shakuwar na da karfi."

asmeebridalzone ta ce:

"Ayyah, wannan kukan lokacin da zai zo, ba za ki sani ba."

sos_kitchen ta ce:

"Tarihi , Allah ya jikan iyaye, ya haskaka masu kabarin su. (Ameen) ❤️."

mammamia8477 ta ce:

"A fasa auren mana ta zauna abinta a gida, ko auren dole ne?"

useee_ey ta ce:

"Wayyo Allah. Allah basu zaman lafiya."

Bidiyoyin Shagalin Dinan Kyakkyawar Diyar Sanata Sahabi

A baya mun kawo cewa ana ci gaba da shagalin biki a gidan sanata mai wakiltan yankin Zamfara ta arewa, Sanata Sahabi Ya’u.

Kyakkyawar diyar sanata, Amina Ummi c eke shirin shiga daga ciki tare da angonta Muhammad Auwal wanda ya kasance Majikiran Adamawa.

A ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta ne aka gudanar da wani kasaitaccen liyafar dina na bikin amarya amina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel