Kyawawan Hotunan Daurin Auren Wasu Yan Najeriya A Dubai Ya Yadu, Sun Yi Shaglin Bikinsu A Saukake

Kyawawan Hotunan Daurin Auren Wasu Yan Najeriya A Dubai Ya Yadu, Sun Yi Shaglin Bikinsu A Saukake

  • Wani dan Najeriya, Duru C.E. ya yada kyawawan hotunan auransa da aka yi a saukake a Hadaddiyar Daular Larabawa
  • Koda dai ya ce gagarumin biki na nan zuwa a gaba, masu amfani da Twitter da dama sun lura da rashin mutane a sha’anin
  • Duru, wanda ke zana gine-gine ya auri kyakkyawar matarsa wanda yace sun shafe tsawon shekaru biyar suna soyayya

Dubai - Wani dan Najeriya mai suna Duru C.E. ya angwance da kyakkyawar budurwarsa a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Sai dai wasu mutane sun lura cewa babu wasu baki da suka halarci daurin auren yayin da aka gano mutumin tare da matarsa kadai a wajen karbar takardar shaidar zama ma’aurata.

Mata da miji
Kyawawan Hotunan Daurin Auren Wasu Yan Najeriya A Dubai Ya Yadu, Sun Yi Shaglin Bikinsu A Saukake Hoto: @thesignature01.
Asali: Twitter

Gagarumin biki na nan zuwa a gaba

Sai dai kuma, Duru ya ce akwai gagarumin shagalin bikin da zai zo a nan gaba bayan masu amfani da Twitter sun fara sharhi game da yadda ya yi bikinsa cikin sauki baki a lekun daga shi dai amaryarsa.

Kara karanta wannan

Aure Yakin Mata: Bidiyon Yadda Diyar Sanata Sahabi Ta Rungume Mahaifinta Cikin Kuka Yayinda Za a Kaita Dakinta

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Duru, sun kwashe tsawon shekaru 5 suna soyayya da amaryar tasa kafin suka shiga daga ciki a wani taro da aka yi a kasar Dubai.

Yayin da yake yada hotunan, Duru ya ce:

“Bayan shekaru 5 ana abota, gami da shekaru 3 na soyayya, a karshe mun shiga daga ciki, a kotun Hadaddiyar Daular Larabawa. Zan shafe sauran rayuwata tare da sahibata.
“Ina mika godiyata ga abokai da yan uwa (A ciki da wajen Twitter) wadanda a koda yaushe suke kasancewa tare da mu. Babban shagalin bikin na nan a gaba kuma za mu sanar da ranar a lokacin da ya kamata.”

Kalli wallafar tasa a kasa:

Kyawawan Hotunan Daurin Auren Wasu Yan Najeriya A Dubai Ya Yadu, Sun Yi Shaglin Bikinsu A Saukake

Jama’a sun yi martani

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An gano gawarwakin wasu adadi na mutanen da suka mutu a benen Abuja

@AbiolaYuusuf ya ce:

“Wani misali da ke nunawa nmutane cewa za ka iya yin biki a saukake kuma a zauna lafiya. Ba dole sai mutum ya takura kansa da aljihunsa ba.”

@iam_lina1 ta yi martani:

"Ina mai taya ku murna. Allah ya albarkaci sabon gidanku kuma tuni kun ginasa a kan tafarkin Ubangiji. Ban san ku ba amma na tayaku murna kuma na ji dadin wannan sabon tafiya taku. Allah ya sadaku da tarin farin ciki, zaman lafiya da tarin jin dadi.”

Bidiyoyin: Yadda Matasa Suka Yi Ruwan Liki Harda Su Daloli A Wajen Shagalin Dinan Dan Sarkin Kano

A wani labarin, mun ji cewa a ranar Juma’a, 26 ga watan Agusta ne dubban jama’a suka shaida daurin aure tsakanin Kabiru Aminu Bayero, dan sarkin Kano Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, da kyakkyawar amaryarsa Aisha Ummaran Kwabo.

Duk a cikin shagalin bikin, an gudanar da wani kasaitaccen liyafar Dina wanda ya samu halartan amarya da ango.

Kara karanta wannan

Bidiyoyin Shagalin Dinan Kyakkyawar Diyar Sanata Sahabi

Kamar yadda aka saba, yan uwa da abokan sabbin ma'auratan sun yi masu kara wajen kasancewa a taron.

Asali: Legit.ng

Online view pixel