Bidiyoyin Shagalin Dinan Kyakkyawar Diyar Sanata Sahabi

Bidiyoyin Shagalin Dinan Kyakkyawar Diyar Sanata Sahabi

  • Shagalin bikin diyar Sanata Sahabi Ya’u, Amina Ummi da angonta Muhammad Auwal (Majikiran Adamawa) na ci gaba da gudana
  • An gudanar da wani kasaitaccen dinan bikin a ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta, a wani katafaren dakin taro
  • Bidiyoyin shagalin sun yadu a shafukan soshiyal midiya inda amarya Ummi da kawayenta suka fito shar da su

Zamfara - Ana ci gaba da shagalin biki a gidan sanata mai wakiltan yankin Zamfara ta arewa, Sanata Sahabi Ya’u.

Kyakkyawar diyar sanata, Amina Ummi c eke shirin shiga daga ciki tare da angonta Muhammad Auwal wanda ya kasance Majikiran Adamawa.

Dinan diyar sanata Sahabi
Bidiyoyin Shagalin Dinan Kyakkyawar Diyar Sanata Sahabi Hoto: fashionseriesng
Asali: Instagram

A ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta ne aka gudanar da wani kasaitaccen liyafar dina na bikin amarya amina.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Aka Biya Dala 20,000 Kudin Kamun Diyar Sanata Sahabi

An gudanar da dinan ne a cikin wani katafaren dakin taro da aka yiwa ado na musamman yayin da ko ina ya cika da haske da walwali.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amarya Amina ta sanya wani hadadden doguwar riga irin na amaren zamani wanda aka yiwa kwalliya da duwatsu yayin da kanta ke daure da kallabi, ta fito shar da ita cikin kamala.

A cikin bidiyoyin da shafin fashionseriesng an gano kawayen amarya sanye da dogayen riguna launin shudi masu duhu suna kwasar rawa kuma duk sun hadu matuka.

Hakazalika a daya daga cikin bidiyoyin, an gano sanda uwar amarya ta shigo dakin taron tare da mukarrabanta wadanda suke take mata baya.

Kalli bidiyoyin a kasa:

Bidiyo: Yadda Aka Biya Dala 20,000 Kudin Kamun Diyar Sanata Sahabi

A baya mun kawo cewa kamar yadda yake bisa al’adar mallam Bahaushe a duk lokacin da ake bukukuwan aure, a kan yi kamun amarya inda dangin ango za su biya kawayen amarya wasu yan kudade kafin su barsu su ganta.

Kara karanta wannan

Hotuna da Bidiyon shagalin Kamun diyar Sanata Sahabi Yau sun Dauka Hankali

Hakan ce ta kasance a wajen shagalin kamun kyakkyawar diyar sanata Sahabi Ya’u mai wakiltan Zamfara ta arewa.

Dangin ango Muhammad Auwal sun isa dakin taron inda kawayen amarya Amina Ummi suka nemi a biya dala 10,000 don amaryar tasu mai tsada ce.

Sai dai kuma dangin angon sun nuna cewa dansu mai tsada ne don aka suka biya kudin kamu dala 20,000 wanda ya yi daidai da naira 8,431,600.00 kudinmu na gida Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel