Yadda Saurayi Ya Guji Budurwarsa Saboda Gano Ta Kama Sana’ar Siyar da Kifi

Yadda Saurayi Ya Guji Budurwarsa Saboda Gano Ta Kama Sana’ar Siyar da Kifi

  • Wata kyakkyawar budurwa ta ba da labarin ta da yadda ta rabu saurayinta saboda ta kama sana'ar tallan kifi
  • A cewarta, saurayin nata ya gaza jure yadda ta sauke ajin ta, ta kama sana'ar da take ganin zai cece ta daga roko
  • Bayan ganin bidiyon nata, 'yan TikTok sun yaba mata, sun kuma yi mata fatan samun nasara a abubuwan da ta sa a gaba

Wata kyakkyawar budurwa ta shiga jerin bidiyon kalubale, inda ta bayyana dalili da yadda ta rabu da wani saurayinta da ya nuna zai i watsi da ita.

Da take bayani a TikTok, budurwar ta ce saurayin nata ya gudu ne saboda kawai ta fara sana'ar tallan kifi.

Saurayi ya guji budurwarsa saboda kama tallan kifi
Yadda saurayi ya guji budurwarsa saboda gano tana tallan kifi | Hoto: TikTok/@springfoods_.
Asali: UGC

Budurwar ta ce sam ba a yin ta mutane a rayuwa, kuma kowa da irin abin da ya zabar ma kansa. Ta ce a yanzu dai ta habaka, domin ta kai ga gina kasuwancin kasa da kasa ta sanadiyyar siyar da kifi.

Kara karanta wannan

N30k Kacal na Kashe: Bidiyon Siyayya Raga-raga da 'Yar Najeriya Tayi a UK ya Bada Mamaki

Ta yada wasu hotuna biyu da suka nuna rayuwar ta baya da kuma a yanzu. A daya daga cikin hotunan, an gan ta dauke da buhunnan kifi a ka, a daya kuwa, an ganta zaune a ofis tana shan AC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin 'yan TikTok

'Yan TikTok sun yi ca kan wadannan hotuna, sun tofa albarkacin bakinsu. Ga dai kadan daga ciki

@May ta ce:

"Cin gagaruwar nasara itace mafi kyawun fansa."

@LummyEmpire ya ce:

"Yanzu kuma kin zama Jagaban maimasu siyar da dodon kodi."

@benitapaul3031 ya ce:

"Tsaya kem kan akan ra'ayinki ba tare da waiwaye ba shine mafi kyan abu."

@favouratta yace:

"Wannan abin sha'awa ne matuka, Allah ya kara miki girma da daukaka."

@Smart Onyeukwu yace:

"Wannan shine mafi kyan sigar kalubale da na gani."

@Nifemi446 yace:

"Wannan shi muke kira da canji kenan."

Wata 'yar Najeriya ta nuna yadda take sana'ar POP, jama'a sun shiga mamaki

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Budurwa Mai Digiri ta Koma Siyar da Kayan Miya, Bidiyo Ya ba Jama'a Mamaki

A wani labarin, wata 'yar Najeriya mai suna Okeke Stephanie, ta ba da mamaki yayin da ta bayyana irin sana'ar da take yi don samun na kashewa.

Stephenie dai 'yar jihar Delta ce, kuma ta ce ta kama sana'ar daben saman daki na POP ne domin ta kashe kwarkwatar da ke kanta.

Ta kuma bayyana cewa, ta kan sha suka da zolaya game da wannan aikin da take yi, inda wasu ke cewa aiki ne na maza.

Asali: Legit.ng

Online view pixel