Kyakkyawar Budurwa Mai Digiri ta Koma Siyar da Kayan Miya, Bidiyo Ya ba Jama'a Mamaki

Kyakkyawar Budurwa Mai Digiri ta Koma Siyar da Kayan Miya, Bidiyo Ya ba Jama'a Mamaki

  • Wata kyakyawar budurwa da ta kammala digirinta a fannin kimiyyar ruwa ta bayyana cewa yanzu ta zama 'yar kasuwa
  • Budurwar ta bayyana a bidiyo cike da murmushi inda take zubawa kwastoma kayan miya duk da digirin da take da shi
  • Wasu jama'a sun yi martani kan bidiyon inda suka bayyana cewa akwai mutane da yawa dake fuskantar irin abinda take fuskanta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata matashiyar budurwa wacce ta kammala digiri a fannin kimiyyar ruwa ta shiga gasar TikTok inda mutane ke bayyana abinda suka karanta a makaranta da kuma sana'ar da suka koma daga baya.

A bidiyon da ta wallafa, an ga budurwar tana murmushi sanye da rigar kammala digiri yayin da ta karkace tana daukar hoto da mahaifiyarta.

Budurwa
Kyakyawar Budurwa Mai Digiri ta Koma Siyar da Kayan Miya, Bidiyo Ya ba Jama'a Mamaki. Hoto daga TikTok/@shah20216
Asali: UGC

Mai digiri ta koma 'yar kasuwa

Wani bidiyonta kuwa ya nuna kyakyawar budurwar da ta kammala digirin tana siyar da kayan gwari kamarsu albasa, tumatir da sauransu a kasuwa.

Kara karanta wannan

So Nake su Koyi Sana'a da Tattali: Mata Mai Gidan Gona ta ba Yaranta Aiki, Albashinsu 105k a Sati

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kasuwar, budurwar ta bayyana sanye da gilashi yayin da take cigaba da murmushi yayin da take zuba kayan miya cikin leda.

Jama'a sun yi martani

A yayin rubuta wannan rahoto, bidiyon ya tara sama da tsokaci 300 tare da jinjina sama da 27,000.

Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin martanin.

user3232987758582 yace:

"A kalla kin yi kyau da kike sana'ar."

Brian_thomas yace:

"Ga mutanen dake karanta kimiyyar ruwa, kada ku damu. Kowa yana da labarinsa mabanbanci. Ni a bangarena, na samu aiki tun kafin in kammala karatuna."

ODZZ yace:

"Abun sha'awar shi ne kina bayyana halin da kike ciki har sai komai ya daidaita."

Javan Matamano yace:

"Ki yarda da Ubangiji, lokaci na zuwa. Ubangiji yayi miki albarka."

Sana'a da Tattali: Mata Mai Gidan Gona ta ba Yaranta Aiki, Albashinsu 105k a Sati

Kara karanta wannan

Ya Rabu Dani Saboda Ina Da Muni: Hotunan Sauyawar Wata Budurwa Shekaru Bayan Saurayi Ya Guje Ta Ya Ba Da Mamaki

A wani labari na daban, Kimoi Jerotich, wata mata mai yara uku ta bai wa jama'a mamaki bayan wasikar daukar aikin da tayi wa yaranta biyu ta bayyana.

A wasikar da ta yadu a soshiyal midiya, Jerotich ta dauka Shawn mai shekaru shida da Ryan mai shekaru tara aikin shekaru uku kacal.

A yayin tattaunawa da kafar yada labaran Kenya ta Tuko.co.ke, HRM tayi bayanin cewa ta yanke wannan hukuncin ne saboda tana son shirya yaranta saboda gaba da wuri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel