N30k Kacal na Kashe: Bidiyon Siyayya Raga-raga da 'Yar Najeriya Tayi a UK ya Bada Mamaki

N30k Kacal na Kashe: Bidiyon Siyayya Raga-raga da 'Yar Najeriya Tayi a UK ya Bada Mamaki

  • Wata budurwa 'yar Najeriya mai suna Chidera Stephen, dake rayuwa a Ingila ta fitar da wani bidiyo na yawan kayan da ta samu a dubu talatin
  • Babu shakka Chidera ta janyo cece-kuce saboda wasu sun ce ko rabin yawan kayan da ta siyo ba zasu samu a kasuwar Najeriya ba
  • Wasu kuwa cewa suka yi saboda Ingila ce, amma a wasu kasashen ma kayan da za a samu a N30,000 a Najeriya masu yawa ne sosai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata budurwa 'yar Najeriya dake rayuwa a kasar waje mai sun Chidera Stephen, ta bayyana yawan kayan da ta siya a wani kanti a Ingila da N30,000 a wani bidiyon TikTok.

A yayin nadar bidiyon kayan, budurwar ta siya abubuwan da suka hada da fakitin naman kaji, abubuwan sha, kayan marmari da sauransu.

Budurwa Taje Kasuwa
N30k Kacal na Kashe: Bidiyon Siyayya Raga-raga da 'Yar Najeriya Tayi a UK ya Bada Mamaki. Hoto @chiderastephen
Asali: UGC

Kasa da N2000 aka siya kaza

Fakitin fuka-fukan kaza a siye shi kasa da N2,000 karam yarra farashin ya nuna. Ya danganta da nawa ake canjin fam daya, abinda ta kashe a naira bai kai N30,000 ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalla bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin martanin jama'a

Xage yace:

"Fam 40 kamar wurin N32,000 ne a Najeriya

Queen Queen tace:

"Abinci basi da tsada a Ingila... Ina yawan fadawa mutane, a Najeriya dubu ashirin ba za ta ritsa maka abincin mako daya ba."

Dunni tace:

"Eyyeh, Mako biyu kace. A gaskiya lokaci yayi da zan bar kasar nan."

surrybala1 tace:

"A Najeriya za ka iya samun fiye da wannan a fam 40."

Kyakkyawar Budurwa Mai Digiri ta Koma Siyar da Kayan Miya, Bidiyo Ya ba Jama'a Mamaki

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa wacce ta kammala digiri a fannin kimiyyar ruwa ta shiga gasar TikTok inda mutane ke bayyana abinda suka karanta a makaranta da kuma sana'ar da suka koma daga baya.

A bidiyon da ta wallafa, an ga budurwar tana murmushi sanye da rigar kammala digiri yayin da ta karkace tana daukar hoto da mahaifiyarta.

Wani bidiyonta kuwa ya nuna kyakyawar budurwar da ta kammala digirin tana siyar da kayan gwari kamarsu albasa, tumatir da sauransu a kasuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel