Wata 'yar Najeriya ta nuna yadda take sana'ar POP, jama'a sun shiga mamaki

Wata 'yar Najeriya ta nuna yadda take sana'ar POP, jama'a sun shiga mamaki

  • Wata kyakkyawar mace ‘yar Najeriya mai suna Okeke Stephanie ta ba da mamaki yayin da ta bayyana sana'ar da ta ke yi
  • Stephanie dai ta kama sana'ar POP ne, lamarin da wasu ke ganin ba sana'a ce da ta dace diya mace ba
  • Sai dai, ta bayyana irin kwarin gwiwar da take dashi, da kuma kalubalan da ta kawar kafin kai wa ga hakan

Jihar Delta - Wata 'yar Najeriya mai suna Okeke Stephanie, ta ba da mamaki yayin da ta bayyana irin sana'ar da take yi don samun na kashewa.

Stephenie dai 'yar jihar Delta ce, kuma ta ce ta kama sana'ar daben saman daki na POP ne domin ta kashe kwarkwatar da ke kanta.

Ta kuma bayyana cewa, ta kan sha suka da zolaya game da wannan aikin da take yi, inda wasu ke cewa aiki ne na maza.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Tsoho mai shekaru 66 ya kama tallan mangoro don tara kudin maganin matarsa

Yadda mace ta kama sana'ar POP, ta ba da mamaki
Ina alfahari da sana'ata: 'Yar Najeriya da ke sana'ar daben saman daki na POP ta magantu | Hoto: BBC Pidgin / Afoma82
Asali: Instagram

A cewar Stephanie, ba jama'ar gari kadai ba, har iyayenta ba su nuna farincinsu ga wannan sana'a ta yin POP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da haka, ta tattara hankalin wuri guda, inda ta tabbatar da ta koyi sana'ar yadda ya dace har kowa ya yarda ita kwararriya ce.

A cewarta, duk da sana'ar na sanya a ganta futu-futu, duk da hakan tana iya shiga mai kyau idan ta ji sha'awar caba kwalliya.

Matsalolin da take fuskanta

Stephenie ta koka da yadda wasu ke mata ganin wacce ta kama sana'ar da bata cancanci diya mace ba.

Wasu kuwa kallo suke ba ma za ta iya yin aikin yadda ya kamata ba kasancewar ita ba namiji bace.

Duk da haka, ta ce ita fa a kan gaba take wurin aikinta, domin kuwa duk wanda ta zauna ta cancarawa aiki sai ya yaba kuma tana yin iya kokarinta.

Kara karanta wannan

Bayan Shekaru 16 da Aure, Magidanci Ya Fattaki Matarsa, Ya Aure Mai Gidan Haya Don Morar Hayar Kyauta

Yabo daga jama'ar intanet

Abiolaamao ya ce:

"Najeriya tana da tarin masu basira, Ya Allah azurtamu da shugabanci na gari."

Jasonsfoodsng ne ya ce:

"Ki tafi kawai yarinya, Allah ya albarkaci sana'arki ta hannu, ya kuma cika miki burin rayuwarki."

Ochonojone ya rubuta:

"Ga kyau ga kuma aiki tukuru."

Ib.flora ya ce:

"Kai, abun burgewa! 'Yar uwa abu ya yi kyau."

Ogesbakedtreats ya ce:

"Aiki dai aiki ne kawai, sannu da aiki 'yar uwa."

Bidiyon Yadda Wani Tsoho Mai Shekaru 66 da Ke Tallan Mangoro ke Nemawa Matarsa Kudin Magani

A wani labarin, wani tsoho mai shekaru 66 dan kasar Ghana mai suna Isaac Antwi da ke tallan mangoro ya bayyana irin gwagwarmayar rayuwa da yake fama da ita, kana ga tsananin talauci.

Ya bayyana hakan ne a a wata hira da Crime Check TV GH, inda ya bayyana cewa ya kama sana'a ne tun lokacin da ya bar makaranta ya dukufa da neman kudi bayan rasuwar mahaifinsa.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Hana Mahaifiyarsa Shiga Gida Saboda Yanayin Shigarta, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Antwi ya tuna cewa, a baya ya taba zuwa Najeriya ko zai samu canjin rayuwa, amma ya ga abubuwa kamar ana karawa wuta fetur. Daga baya ya sake dawowa Accra a kasar Ghana, nan ma dai babu abin da ya sauya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel