An Kama Mutumin Da Ya Lakaɗa Wa Jami'in Ɗan Sanda Duka A Legas

An Kama Mutumin Da Ya Lakaɗa Wa Jami'in Ɗan Sanda Duka A Legas

  • Yan sanda sun kama wani mutum mai suna Billy King Tokunbo da ake zargi da saba dokan hanya da yi wa dan sanda duka
  • SP Benjamin Hundeyin, mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Legas ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a
  • Hundeyin ya ce an kuma kama motar wanda ake zargin kirar Toyota Corolla sannan za a gurfanar da shi a kotu da zarar an kammala bincike

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Legas - Runduna Yan sandan Najeriya reshen Jihar Legas ta tabbatar kama wani mutum mai suna Billy King Tokunbo kan yi wa dan sanda duka da kuma saba dokar hanya.

Kakakin rundunar yan sandan Legas SP Benjamin Hundeyin ne sanar da hakan a shafinsa na Twitter, a ranar Juma'a yana mai cewa an nadi bidiyon mutumin yana dukan dan sanda.

Wanda ake zargi
An Kama Mutumin Da Ya Lakada Wa Jami'in Dan Sanda Duka A Legas. Hoto: @BenHundeyin.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwar na Hundeyin tana dauke da faifan bidiyo da ke nuna wanda ake zargin ya damke dan sandan da ke sanya da kayan aikinsa da bindiga a bayansa.

Hundeyin ya rubuta:

"Nan take aka kama wand ake zargin, Billy King Tokunbo, wanda ya yi tuki a barauniyar hanya.
"An kuma kama motarsa kirar Toyota Corolla mai lamba LSR 430 FT nan take. Za a gurfanar da shi saboda saba dokokin hanya da suka dukan jami'in dan sanda."

Shima a martaninsa kan dukan jami'in, kakakin yan sanda, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya yi tir da abin da aka aikata inda wasu marasa bin doka cikin mutane suke dukan yan sanda.

A rubutun da ya yi a shafinsa na Twitter, Adejobi ya ce:

"A yayin da muke dagewa sosai don mutunta mutane da kare hakkokinsu, mu kanmu ya kamata a rika mutunta mu."

An Kama Hatsabibin Dan Bindiga, Yusuf Monore, Dan Shekara 20 A Kaduna

A wani rahoton, yan sanda a Jihar Kaduna sun kama wani dan bindiga mai shekara 20 dauke da bindigu AK-47 guda biyu a garin Galadimawa a karamar hukumar Giwa, rahoton Channels TV.

Kakakin yan sandan Kaduna, DSP Mohammed Jalige, cikin sanarwar da ya fitar ya ce yan sandan Operation Restore Peace ne suka kama shi.

Ya ce yan sandan, bayan samun bayanan sirri, sun kai samame sansanin yan bindiga a dajin Galadimawa suka yi musayar wuta da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel