'Yan Sanda Sun Cafke Sojojin Bogi 2 a Legas Dauke da Layu da Makamai

'Yan Sanda Sun Cafke Sojojin Bogi 2 a Legas Dauke da Layu da Makamai

  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kamen wasu sojojin bogi 2 a Legas
  • Kamar yadda ya bayyana, an yi ram da daya daga cikinsu ne yayin da ake dabbaka dokar haramcin yawon babura a wasu sassan jihar
  • An kama sojojin bogin da kayan sojoji, 'yan sanda, layoyi, harsasai masu rai guda 9 kuma ana binciken ta'addancin da suke tafkawa

Legas - Rundunar 'yan sandan jihar Legas tace ta cafke wasu sojan bogi biyu a jihar. Kakakin rundunar 'yan sandan, Benjamin Hundeyin, yace an same shi da kayan sojoji, 'yan sanda, layu da harsasai masu rai.

A wata takarda da ya fitar, Hundeyin yace Oluwatosin Gabriel, daya daga cikin wadanda ake zargin, ya shiga hannu ne yayin da ake dabbaka dokar haramcin yawon babura a wasu sassan jihar, TheCable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Manyan 'Yan Ta'adda 8 Sun Shiga Hannun Dogaran Fadar Shugaban Kasa a Abuja

Fake Soldiers
'Yan Sanda Sun Cafke Sojojin Bogi 2 a Legas Dauke da Layu da Makamai. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Yace 'yan sanda suna binciken kwakwaf wanda hakan ya kai ga kama Nurudeen Agboola, wanda ake zargi na biyu wanda shi ke samar da kayan sojojin.

Premium Times ta rahoto cewa, yace abubuwan da aka samo daga sojan bogin da me samar masa da kayayyakin sun hada da kayan sojoji hudu, harsasai masu rai tara, I.D Card na sojoji, kayan 'yan sanda da layoyi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ana cigaba da bincike kan yawan ta'addancin da suka tafka. Za a gurfanar da wadanda ake zargin bayan an kammala bincike," yace.

Ya kara da cewa, Abiodun Alabi, kwamishinan 'yan sandan jihar, ya jinjinawa jami'an kan kokarinsu.

Manyan 'Yan Ta'adda 8 Sun Shiga Hannun Dogaran Fadar Shugaban Kasa a Abuja

A wani labari na daban, rundunar sojin Najeriya ta kai samame maboyar 'yan ta'adda inda suka cafke manyan 'yan ta'adda takwas a yankin.

Kara karanta wannan

Hotunan Mayakan Kasar Waje Masu Alaka Da Boko Haram Da Aka Kama A Benue

Hedkwatar tsaro ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Augustan 2022 inda ta kara da cewa an kama 'yan ta'addan ne a maboyarsu dake Deidei Abbatoir da kauyen Dukpa a karamar hukumar Gwagwalada, The Nation ta rahoto.

Dakarun fadar shugaban kasan ne suka aiwatar da aikin. Idan za a tuna, hafsoshin soji biyu da sojoji shida daga cikin dogaran fadar shugaban kasan sun rasa rayukansu sakamakon harin kwanton bauna da 'yan ta'adda suka kai yankin Bwari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel