Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Hallaka Insufektan Yan Sanda a Jihar Legas

Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Hallaka Insufektan Yan Sanda a Jihar Legas

  • Wasu miyagun yan bindiga sun tare Jami'in ɗan sanda da ya kai matsayin Insufekta sun harbe shi har lahira a jihar Legas
  • Rundunar yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin mai magana da yawunta, Benjamin Hundeyin, ranar Alhamis
  • Ya ce Marigayin ya baro wurin aikin da nufin zuwa wani wuri yayin da aka farmake shi aka harbe shi har lahira da yammacin Laraba

Lagos - Rundunar yan sanda reshen jihar Legas ta tabbatar da cewa wasu yan bindiga sun kashe Insufektan yan sanda ranar Laraba a yankin Coker Aguda a jihar.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan, Benjamin Hundeyin, ya shaida wa hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ranar Alhamis a Legas cewa Jami'in na cikin Keke-Napep lokacin da maharan suka bindige shi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Rikicin addini ya barke tsakanin kirista da 'yan gargajiya, an kashe wani

Ta'addancin ƴan bindiga.
Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Hallaka Insufektan Yan Sanda a Jihar Legas Hoto: vanguardngr
Asali: Twitter

Kakakin yan sandan ya ce tuni rundunar ta kaddamar da bincike kan lamarin domin bin sawu tare da cafke yan bindigan, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Wane matakin rundunar yan sanda ta ɗauka?

Hundeyin ya ce sun kama Direban Keke-Napep ɗin domin amsa wasu tambayoyi amma daga baya sun sake shi da sharaɗin zai dawo ranar Alhamis domin taimaka wa yan sanda kan binciken da suke yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kakakin yan sandan ya ƙara da cewa an tura Mamacin ya yi aiki a wani Banki, amma kaddarar da ta yi ajalinsa ba ta faɗa masa lokacin da yake wurin aikin ba.

"Ya baro wurin aikinsa domin zuwa wani wuri a cikin Keke mai kafa uku. Ya ɗauki shatar Keken ne kuma shi kaɗai ne fasinja a ciki."
"Ba zato aka farmake shi, aka harbe shi, sannan suka yi awon gaba da bindigarsa ta aiki. Lamarin ya auku da yamma kusan ƙarfe 3:00, ya rasu da daren ranar."

Kara karanta wannan

Yadda Jami’an Yan Sanda Suka Je Har Wajen Shagalin Biki Suka Kama Amarya Kan Zargin Sata

- Benjamin Hundeyin.

Kakakin yan sandan ya ce ba zasu saki bayanan Mamacin ba har sai sun tuntuɓi iyalansa, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Harbe Hadimin Jigon APC Har Lahira a Wurin Shagalin Karin Shekara

Wasu mahara sun farmaki wurin bikin karin shekara a Legas, sun bindige hadimin shugaban ƙaramar hukuma har Lahira.

Kakakin yan sandan jihar Legas ya tabbatar da cewa harbin bindiga ne ya yi ajalin mutumin a a Asibiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel