An Kama Hatsabibin Dan Bindiga, Yusuf Monore, Dan Shekara 20 A Kaduna

An Kama Hatsabibin Dan Bindiga, Yusuf Monore, Dan Shekara 20 A Kaduna

  • Yan sanda a Kaduna sun kai samame wani sansanin yan bindiga a garin Galadimawa a karamar hukumar Giwa
  • DSP MOhammed Jalige, kakakin yan sandan Kaduna ya ce sun yi nasarar kama Yusuf Monore, dan bindiga mai shekara 20 da bindigun AK-47 da harsashi da wayoyi
  • Yan sandan sun kuma yi nasarar tarwatsa sansanin yan bindigan bayan musayar wuta da suka yi inda bata garin suka tsere da raunin bindiga

Jihar Kaduna - Yan sanda a Jihar Kaduna sun kama wani dan bindiga mai shekara 20 dauke da bindigu AK-47 guda biyu a garin Galadimawa a karamar hukumar Giwa, rahoton Channels TV.

Kakakin yan sandan Kaduna, DSP Mohammed Jalige, cikin sanarwar da ya fitar ya ce yan sandan Operation Restore Peace ne suka kama shi.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Bindige Jami'an Yan Sanda 2 Har Lahira A Jihar Plateau

Taswirar Jihar Kaduna.
An Kama Dan Bindiga Dan Shekara 20 Dauke AK-47 Biyu Da Harsashai A Kaduna. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce yan sandan, bayan samun bayanan sirri, sun kai samame sansanin yan bindiga a dajin Galadimawa suka yi musayar wuta da su.

Yan bindigan, ya ce, sun tsere cikin dajin da raunin harsashin bindiga daban-daban.

A cewar kakakin yan sandan, jami'an sunyi nasarar kama daya cikin yan bindigan, Yusuf Monore, dan shekara 20 dauke da AK-47 guda biyu da harsashi da wayoyin salula.

Jalige ya ce a yanzu ana yi wa wanda ake zargin tambayoyi sannan ana bin sahun sauran da suka tsere, Channels TV ta rahoto.

Kwamishinan yan sanda ya yaba wa jami'an da suka kai samamen

A bangarensa, kwamishinan yan sandan Jihar, Yekini Ayoku ya jinjinawa dakarun da suka kai samamen sannan ya basu tabbacin cigaba da samun goyon bayansa.

Ya kuma bukaci mazauna Kaduna su cigaba da sanya ido sannan su kai rahoton duk wani abin da ba su gamsu da shi ba wurin hukumomin tsaro.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Kai Samame Sansanin Rikakken 'Dan Bindiga Lawal Kwalba, Sun Kwato Kayan Hada Bama-bamai

An Cafke Matar Ɗan Fashin Daji a Jihar Katsina Da N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta

A wani rahoton, yan sanda a Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekara 27 dauke da kudi N2.4m na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.

An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a lokacin da ta ke shirin hawa babur din haya daga Batsari zuwa Nahuta.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel