‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Basarake a Kudancin Najeriya a Cikin Jirgi

‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Basarake a Kudancin Najeriya a Cikin Jirgi

  • Al’umma sun kidime a halin yanzu domin sun ji labari Sarkin kasar Abissa, Mai martaba Matthew Opoto yana hannun ‘yan bindiga
  • Mai martaba Matthew Opoto ya dawo daga wata tafiya zai koma garin Abissa, ‘Yan bindiga suka biyo tawagarsa a jirgi, suka sace shi
  • Tun da aka yi gaba da Shugaban Majalisar Sarakunan na karamar hukumar Akuku Toru a Ribas, ba a sake jin duriyarsa ba har yau

Rivers - A wani rahoto mara dadi da Daily Trust ta fitar a ranar Litinin, 22 ga watan Agusta 2022, an ji cewa an sace Sarki Matthew Opoto a jihar Ribas.

Mai martaba Matthew Opoto wanda shi ne shugaban Sarakunan gargajiya na Abissa a karamar hukumar Akuku Toru a Ribas, ya shiga hannun miyagu.

Kara karanta wannan

Na Bar Koyarwa Har Abada Idan Aka Hana Mu Albashin Watanni 6 Inji Malamin Jami’a

Rahoton yace an dauke Mai martaban ne yana cikin jirgin ruwa a hanyarsa ta komawa kasarsa. Tun dai lokacin ba a sake jin duriyar Sarkin ba.

Wasu miyagun ‘yan bindiga a cikin jirgin ruwa mai inji suka zo, suka dauke Mai martaba Matthew Opoto yayin da su kuma ke tafiya a kwale-kwale.

Wata majiya ta shaidawa 'yan jarida cewa Mai martaban zai koma garin Abissa tare da wasu manyan kasa da ke tare da shi a lokacin da abin ya faru.

Bayan ‘yan bindigan sun gane Basaraken a tawagarsa a kwale-kwalen, sai suka kinkimo shi, suka jefa sa a jirgin da suka zo da shi, suka yi gaba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dakarun C41
Jami'an tsaro C41 a Ribas Hoto: @govwike
Asali: Twitter

Yadda abin ya faru - Majiya

Da aka zanta da wani wanda ya fito daga yankin Sarki Matthew Opoto a Fatakwal, ya shaida cewa Mai martaban yana daf da isa gida, aka yi garkuwa da shi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yaudari manoma duk da kulla yarjejeniyar zaman lafiya, sun sace 16

“Mai martaba shugaban sarakunan Abissa, High Chief Mathew Opito yana tafiya da wasu daga cikin ‘yan majalisarsa, saura tafiyar minti biyar ya rasa garinsa, ‘yan bindiga suka zo a jirgin ruwa mai gudu, suka dauko shi, sannan suka yi gaba.”
“Ba mu da wani labari a game da shi. Daukacin al’umma sun shiga zulumi, sarakai, dattawa, matasa da mata duk sun damu, domin an ji shiru.

Wannan mutumi ya yi kira ga jami’an tsaro, sojojin ruwan Najeriya, Pathfinder (NNS Pathfinder), da gwamnatin Ribas su yi kokarin ceto wannan Sarki.

An yi haka - 'Yan Sanda

Mai magana da yawun ‘yan sanda na reshen jihar Ribas, Grace Iringe-Koko ta tabbatar da cewa babu shakka an samu labarin yin gaba da Sarki Opoto.

Grace Iringe-Koko tace ana bakin kokari domin gano wadanda suka yi wannan danyen aiki. The Guardian ta tabbatar da wannan rahoto a yau da safe.

Rikicin kujera a Ebonyi

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun tarfa jigon APC a yankinsu, sun hallakashi

Kun samu rahoto Princess Ann Agom-Eze ta dage sai an ba ta takarar Sanata a APC, wannan ya sa ta zama ‘Yar adawar Gwamnan Ebonyi, David Umahi.

Tun da ta tsaya takara, Ann Agom-Eze tace ta ke ganin kalubale iri-iri, tace a halin yanzu gwamnati ta dakatar da fanshon da ake biyanta a kowane wata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel