'Yan Bindiga Sun Yi Watsi da Yarjejeniyar Zaman Lafiya Yayin da Manoma Suka Fara Girbi a Neja

'Yan Bindiga Sun Yi Watsi da Yarjejeniyar Zaman Lafiya Yayin da Manoma Suka Fara Girbi a Neja

  • Bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan bindiga, manoma a jihar Neja sun sake shiga tashin hankali
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, akalla mutane 16 aka sace yayin da manoma ke shirin girbe amfanin gona
  • Jihar Neja na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya da ke fama da azababben harin 'yan bindiga

Bassa, jihar Neja - Manoma a kananan hukumomin Shiroro, Munya da Rafi a jihar Neja sun shiga damuwa yayin da suke fara shirin girbin amfanin gonakansu.

Rahoton jaridar Daily Trust ya ce, manoman sun shiga tashin hankali ne kan warware yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan bindiga suka yi a daidai lokacin da tumatir masara da rogo suka nuna.

An sace manoma 16 tsakanin ranakun Asabar da Lahadin karshen makon jiya a kananan hukumomin Rafi da Shiroro na jihar.

Kara karanta wannan

Harin Jirgin kasa: 'Dan Uwan Budurwar da Shugaban Yan Bindiga Ke Kokarin Aurawa Kansa Ya Koka

'Yan bindiga sun dawo bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya da manoma a Neja
'Yan bindiga sun yi watsi da yarjejeniyar zaman lafiya yayin manoma suka fara girbi a Neja | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cewar manoman, 'yan bindiga sun ci gaba da kai hare-hare kan jama'a duk da cewa a baya sun yi da wajewar zaman lafiya a lokutan shuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sace limami da wasu mutane 15

Majiya daga karamar hukumar Rafi ta ce, 'yan bindigan sun yi awon gaba da limamin garin Luga, a karamar hukumar da sanyin safiyar ranar Lahadi yayin wani kazamin hari.

Shugaban majalisar matasan Lakpama, Jibrin Abdullahi Allawa ya bayyana cewa, an kuma sace wasu manoma 15 daga yankunan Bassa da yammacin Asabar.

A cewarsa, jama'a da dama, ciki har da mata da kananan yara ne suka yi gudun tsirewa harin na 'yan bindiga.

A cewar Allawa:

“Wasu yankuna sun yi yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan ta'addan domin su samu damar aiki a gonakinsu.
"Amma dai yanzu ‘yan bindigan sun dawo haikan, kuma sun farmaki garin Bassa ido na ganin ido, suka fasa gidaje da shaguna tare da kwashe kayayyaki a ciki.”

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Manoman Zamfara Zasu Yi Zaman Sasanci da 'Yan Bindiga

Da yake neman tallafin gwamnati, Allawa ya nemi a kawo musu daukin gaggawa domin kiyaye al'ummomin yankin daga ta'addancin wadannan 'yan bindigan.

Yadda 'Yan Bindiga Sun Kallafawa Manoman Kaduna Harajin Miliyoyin Naira

A wani labarin, manoman karamar hukumar Birnin Gwari dake jihar Kaduna sun amince zasu biya makuden kudaden da 'yan bindiga suka kallafa musu in har suna son amfani da gonakinsu.

Kamar yadda Ishaq Usman Kasai, shugaban kungiyar masarautar Birnin Gwari, yace 'yan bindigan sun kallafa musu harajin miliyoyin naira kan manoman, Daily Trust ta ruwaito.

A wata takarda, yace manoman sun sun yanke hukuncin yin ciniki da 'yan bindigan saboda basu da wata mafita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel