Hotunan Kafin Aure Na Kyakkyawar Diyar Sarkin Kano, Ruqayya Bayero Da Angonta Amir Kibiya

Hotunan Kafin Aure Na Kyakkyawar Diyar Sarkin Kano, Ruqayya Bayero Da Angonta Amir Kibiya

  • Ruqayya Bayero, kyakkyawar diyar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Bayero zata amarce nan da makonni biyu masu zuwa
  • Amir Kibiya shine zai yi wuff da Ruqayya a ranar Juma’a, 2 ga watan Satumba mai kamawa
  • Kyawawan hotunan kafin aure na masu shirin zama mata da mijin ya karade shafukan soshiyal midiya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Hotunan kafin aure na kyakkyawar diyar sarkin Kano, Ruqayya Aminu Ado Bayero, da angonta sun bayyana a shafukan soshiyal midiya.

Za a dai daura auren Ruqayya Bayero da angonta Amir Kibiya a ranar 2 ga watan Satumba mai zuwa.

Amir da Ruqayya
Hotunan Kafin Aure Na Kyakkyawar Diyar Sarkin Kano, Ruqayya Bayero Da Angonta Amir Kibiya Hoto: fashionseriesng
Asali: Instagram

Duk a cikin shirye-shiryen wannan babbar rana mai zuwa, masu shirin zama ma’auratan sun ware lokaci inda suka sauki kyawawan hotuna a tare.

Kamar yadda shafin fashionseriesng ya wallafa a Instagram, an dauke su hotunan ne a hadaddiyar daular Larabawa wato a kasar Dubai.

Kara karanta wannan

Matar Da Ta Haifi Yan 4 Ta Wallafa Kyawawan Hotunan Lokacin Da Take Goyon Ciki

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Masu shirin zama amarya da angon sun fito shar dasu yayin da suka yi shigarsu ta kamala da kuma yiwa junansu kallon so da kauna.

Kalli kyawawan hotunan a kasa:

Jama'a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin da mutane suka yi kan hotunan nasu a kasa:

seeyah_sagash ta ce:

"Masha Allah yaya❤️."

turarenwuta_arena ta ce:

"Masha Allah sun hadu matuka ❤️❤️."

wan_nyties_and_more ta yi martani:

"MASHA ALLAH."

meemerh___abdul ta ce:

"Masha Allah ❤️."

Zahra Buhari Ta Taya Danuwanta Yusuf Da Matarsa Murnar Cika Shekara Daya Da Aure, Ta Saki Kyawawan Hotunansu

A wani labarin, mun ji cewa shekara ta zagayo da shugaban kasa Muhammadu Buhari da mai martaba sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero suka zama surukai.

Diyar shugaban kasa, Zahra Buhari-Indimi ta taya dan’uwanta, Yusuf da matarsa Zahra Bayero murnar cika shekara daya da aure.

Kara karanta wannan

Doguwar Mace: Bidiyoyin Magidanci Da Santaleliyar Matarsa Sun Haifar Da Cece-kuce, Iya Kugunta Ya Tsaya

Yusuf Buhari da Zahra, diyar sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero, sun yi aure a ranar 20 ga watan Agustan 2021, a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel