Matar Da Ta Haifi Yan 4 Ta Wallafa Kyawawan Hotunan Lokacin Da Take Goyon Ciki

Matar Da Ta Haifi Yan 4 Ta Wallafa Kyawawan Hotunan Lokacin Da Take Goyon Ciki

  • Wata kyakkyawar mata da ke da yara hudu ta wallafa hotunanta don nuna girman cikinta a lokacin da take dauke da juna biyu
  • Matashiyar uwar wacce ta haifi yan hudu ta hadu matuka a cikin hotunan lokacin da take goyon ciki
  • Mabiya shafukan soshiyal midiya sun mato a kan kyawawan hotunan, mata da dama na fatan ina ma ace su haifi yan hudu

Najeriya - Hotunan girman cikin wata yar Najeriya mai dauke da juna biyu ya haifar da martani daga mutane a soshiyal midiya.

Yan shekaru da suka gabata, kyakkyawar matar ta haifi yara yan hudu wadanda aka sanyawa suna Camille, Casper, Carissa, da Casen.

Sunanta ya sha bayyana a kanen labarai bayan ta wallafa kyawawan bidiyoyin yaranta su hudu, kuma wasu mutane sun roki alfarmar ganin hotunta dauke da cikin yaran.

Kara karanta wannan

Na Hadu Da Shi Bai Da Ko Waya: Budurwa Ta Kasance Da Saurayinta Har Ya Siya Motar Benz

ma'aurata da yan hudu
Matar Da Ta Haifi Yan 4 Ta Wallafa Kyawawan Hotunan Lokacin Da Take Goyon Ciki Hoto: @thequadruplet_c4
Asali: UGC

Yan awanni da suka gabata, ta wallafa wani hotonta na lokacin da take dauke da juna biyu, kuma hotunan sun sace zukata a yanar gizo.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Masu amfani da TikTok sun yaba hotunan mahaifiyar yan hudun

@cindyama3 ta ce:

“Na hada kaina da wannan kyakkyawan kyauta.”

@babynanasmum ta ce:

“Wannan ya yi matukar kyau Allah ya albarkaci mijinki da ya tsaya da ita har zuwa yanzu.”

@akyuahberries ta ce:

“Na taya ki murna yar’uwa. Allah ya sadani da irin naki.”

@official_mss ta yi martani:

“Ina fatan samun wannan kyauta ta yan hudu, ta yaya hakan ya faru dan Allah.”

Bidiyon Yadda Lakcara Ta Taya Dalibarta Rainon Jinjirinta Yayin da Take Rubuta Jarrabawa

A wani labarin, wata lakcara da ke sanya idanu kan yadda ake gudanar da jarrabawa ta nuna karamci sosai bayan ta taya wata dalibarta da ke zana jarrabawa kula da jinjirinta.

Kara karanta wannan

Nakuda Mai Tsada: Miji Ya Gwangwaje Matarsa Da Dalleliyar Range Rover Saboda Ta Haifa Masa Da

A cikin wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, an gano lakcarar tana rainon jinjirin dalibar tata cikin yanayi mai ban tausayi.

A cikin dan gajeren bidiyon wanda aka daura a TikTok, an gano lackarar tana zagaye dakin jarrabawar dauke da jinjirin a hannunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel