Bidiyon Yadda Wani Tsoho Mai Shekaru 66 da Ke Tallan Mangoro ke Nemawa Matarsa Kudin Magani

Bidiyon Yadda Wani Tsoho Mai Shekaru 66 da Ke Tallan Mangoro ke Nemawa Matarsa Kudin Magani

  • Wani ma’aikacin jima’i dan kasar Ghana da ke sana’ar sayar da mangwaro don ciyar da kansa da matarsa da ba ta da lafiya ya nemi a taimaka masa.
  • Isaac Antwi, mai shekaru 66, ya mallaki sana’ar matarsa ne bayan da ta yi rashin lafiya, kuma tun yanzu sama da shekara biyu yana sana’ar tasa.
  • Dattijon na fuskantar korar shi daga dakinsa mai cike da rudani kuma yana rokon jama'a da su tallafa masa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Accra, Ghana - Wani tsoho mai shekaru 66 dan kasar Ghana mai suna Isaac Antwi da ke tallan mangoro ya bayyana irin gwagwarmayar rayuwa da yake fama da ita, kana ga tsananin talauci.

Ya bayyana hakan ne a a wata hira da Crime Check TV GH, inda ya bayyana cewa ya kama sana'a ne tun lokacin da ya bar makaranta ya dukufa da neman kudi bayan rasuwar mahaifinsa.

Kara karanta wannan

Bayan Shekaru 16 da Aure, Magidanci Ya Fattaki Matarsa, Ya Aure Mai Gidan Haya Don Morar Hayar Kyauta

Dattijon da ke tallan mangoro don yi wa matarsa magani ya ja hankali
Bidiyon Yadda Wani Tsoho Mai Shekaru 66 da Ke Tallan Mangoro ke Nemawa Matarsa Kudin Magani | Hoto: Crime Check Tv Gh
Asali: UGC

Antwi ya tuna cewa, a baya ya taba zuwa Najeriya ko zai samu canjin rayuwa, amma ya ga abubuwa kamar ana karawa wuta fetur. Daga baya ya sake dawowa Accra a kasar Ghana, nan ma dai babu abin da ya sauya.

Yana neman tamako

A cewar tsohon, ya kama sana'ar da matarsa ke yi sadda take lafiyayya bayan da ta kwanta rashin lafiya. Ga shi ba su da da bare jika, ga kuma tsananin talauci da nasassar mata, lamarin da ya kara cakude masa kenan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan tsoho dai mai suna Antwi na gab da fuskantar kora daga wani tarkataccen dakin da suke rayuwa, don haka ya bayyana cewa yana neman tallafi daga al'ummar da ke ganin za su iya taimaka masa.

Wanda ya tausaya ya ga kuma da halin taimakon wannan bawan Allah, to ga lambar Crime Check TV GH ta WhatsApp 0242074276 domin jin karin bayani game da shi.

Kara karanta wannan

Shin tana kanne: Martanin 'yan Najeriya ga bidiyon wani matashin da ya yi wuff da baturiya

Kalli bidiyonsa:

Yadda Wani Dan Acaba Ya Gamu da Mutumin Kirki, Ya Sauya Shi Zuwa ‘Celebrity'

A wani labarin, wani dan TikTok mai suna @alber_noir, ya yada wani gajeren bidiyo na yadda rayuwar wani dan acaba ta sauya daga cakwalkwali zuwa nasara.

Tun farin faifan bidiyon da aka yada a TikTok, mutumin ya bayyana cewa, shi dai abin da kawai yake dashi a rayuwa ba komai bane face fatan nasara.

A wani sashe na bidiyon kuwa, ya nuna shi fa a baya dan acaba ne, don haka ga ma babur din da yake tare kebura da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel