Bayan Shekaru 16 da Aure, Magidanci Ya Fattaki Matarsa, Ya Aure Mai Gidan Haya Don Morar Hayar Kyauta

Bayan Shekaru 16 da Aure, Magidanci Ya Fattaki Matarsa, Ya Aure Mai Gidan Haya Don Morar Hayar Kyauta

  • Wata mata mai shekaru 39 ta fusata bayan mijinta da suka yi shekaru 16 da aure kwatsam ya fattataketa ba tare da laifin komai ba
  • Matar tace mijinta ya hanzarta aure mai gidan hayan da suke ciki ta yadda zai dinga morar hayar kyauta har karshen rayuwarsa
  • A yayin da rabuwar ma'aurata ba sabon abu bane, a kasar Zambia wannan labarin ya taba zukatan jama'a ba kadan ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata mata 'yar asalin kasar Zambia ta shiga rudani da tashin hankali bayan mijin da suka yi shekaru 16 tare ya koreta daga dakinta kuma ya aure mai gidan hayan da suke ciki.

Maigidan Haya
Bayan Shekaru 16 da Aure, Magidanci Ya Fattaki Matarsa, Ya Aure Mai Gidan Haya Don Morar Hayar Kyauta. Hoto daga ABN TV
Asali: UGC

Trizah Chilanda har yanzu tana cikin firgici kuma bata riga ta kwantar da hankalinta ba bayan da mijinta ya korata gidan iyayenta.

Wani rahoto daga ABN TV ya nuna matar mai shekaru 39 da miji ya kora tana bada labarin matsalar da ta shiga, amma shi yanzu yana morar gidan haya kyauta babu ko sisi.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Hana Mahaifiyarsa Shiga Gida Saboda Yanayin Shigarta, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Kamar yadda matar ta bayyana a bidiyon, ta cika da kunar rai yayin da ma'abota amfani da intanet suka dinga jajanta mata, inda wasu suka dinga mata dariyar halin da ta shiga.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Martanin jama'a

Muzzie Andries Simwatachela:

"Mata su koyi zama masu kudi ba bai matar aure ba kawai. Maza suna son mata masu kudi."

Mbonyiwe Zulu:

"A lokacin da nake girma, kakannina suna da wuraren koyawa mata sana'a a yankunan. A dawo da irin wadannan tsarin domin taimakon mata su tsaya da kafafunsu tare da huce takaici."

Bester Mashabela:

"Maganar gaskiya, namiji ne ya dace ya samar da komai na gida, koda kuwa matar tana samun kudi. Wata rana in har ita ke samarwan sai ta yi korafi. Maza don Allah ku daina gujewa dawainiyarku, mata taimako kawai aka san su da shi."

Kara karanta wannan

Nakuda Mai Tsada: Miji Ya Gwangwaje Matarsa Da Dalleliyar Range Rover Saboda Ta Haifa Masa Da

Bidiyo: Cike da Alfahari, Budurwa Ta Bayyana Saurayinta Kafinta, Ta Rungumeshi Tare da Sumbatarsa

A wani labari na daban, wani bidiyon budurwa 'yar Najeriya tana bayyana saurayinta cike da alfahari ya birge jama'a. Ba saurayin ne da soyayyar bace kadai abun birgewa, har da yadda ta bayyana sana'arsa ta kafinta ba tare da ta kyamacesa ko raina shi ba.

A bidiyon da ta wallafa a TikTok, budurwar ta nadi saurayinta yana tsaka da aiki kuma ta sanar da shi cewa tana bukatar ya rungumeta.

Duk da aikin da yake yi, ya nuna mata hanyar da zata bi ta zo kusa da shi ba tare da ta samu rauni ba. Tana isa wurin da yake, budurwar ta rungume shi tare da sumbatarsa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel