Dan Najeriya Ya Hana Mahaifiyarsa Shiga Gida Saboda Yanayin Shigarta, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Dan Najeriya Ya Hana Mahaifiyarsa Shiga Gida Saboda Yanayin Shigarta, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

  • Wata uwa yar Najeriya da gandareren danta sun haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan sun yi wata yar dirama
  • Cike da barkwanci, matashin ya bukaci mahaifiyar tasa da ta koma inda ta fito saboda yanayin shigarta
  • Da take kare kanta, matar ta nemi sanin wanda ke da gidan tsakanin ita da shi kuma ta fada masa cewa za ta fara cancanrewa da wando

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Bidiyon wani matashi dan Najeriya yana tsokanar mahaifiyarsa cikin raha saboda yanayin shigarta ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

A bidiyon da aka daura a TikTok, matar na shirin gida gida sai dan nata ya hana ta, sannan ya umurci mahaifiyar tasa da ta koma daga inda ta fito.

Mahaifiyar wani dan Najeriya
“Wani Irin Shiga Kika Yi?” Dan Najeriya Ya Hana Mahaifiyarsa Shiga Gida Saboda Yanayin Shigarta, Bidiyo Hoto: TikTok/@omo_mummy
Asali: UGC

Ya ci gaba da martani game dfa yadda bata kwana a gidan kuma sannan ya yi mata fada a kan irin shigar da tayi.

Kara karanta wannan

Shin tana kanne: Martanin 'yan Najeriya ga bidiyon wani matashin da ya yi wuff da baturiya

Matashin ya ci gaba da sukar tumbinta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mahaifiyar tasa ta mayar masa da martani cike da raha cewa ba shine mai gidan ba kuma cewa daga yanzu ma za ta koma saka wando.

Su dukka biyun sun yi magana ne a harshen Yarbanci a cikin bidiyon mai ban dariya inda mutane da dama suka goyi bayan mahaifiyar.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

fatimataderupokok ta ce:

“Duk ba ku ne kuka fadada tumbin ba, dan Allah barta ta wala abunta ko ka sha tsintsiya.”

ibironke 002 ta ce:

“Da alama ya dade da mamarka ta zane ka shiyasa kake kalubalantarta haka.”

soffybee ta ce:

“Uwa mai kyakkyawan diri, ba kaine ka zamar da tumbin haka ba saboda goyon cikinka.”

Omoseke ya ce:

“Zan bi ka saboda mahaifiyarta ina ma ace mahaifiyata na raye nayi irin haka da ita.”

Kara karanta wannan

Bidiyo: 'Saurayina Ya Koma Turai Da Zama Mako 1 Bayan Ya Nemi Aurena', Labarin Wata Budurwa Mai Tsima Zuciya

Nakuda Mai Tsada: Miji Ya Gwangwaje Matarsa Da Dalleliyar Range Rover Saboda Ta Haifa Masa Da

A wani labarin kuma, wata matar aure ta yi nakuda mai tsada bayan maigidanta ya siya mata dankareriyar mota kirar Range Rover 2023 a matsayin tukwicin haifa masa da na uku.

Nizi Rozay ta bayyana cewa sun yi odar tsadaddiyar motar a watan Janairu yayin da ta wallafa hadaddun hotunan dankarariyar abar hawan a shafinta na soshiyal midiya, kuma tuni suka yadu.

Ta wallafa hadaddun hotuna hudu masu sace zuciyar duk wanda ya yi arba da su dauke da rubutu kamar haka:

“A karshe na karbi tukwicin nakudata! Musamman muka yi odarta a watan Janairu kuma a karshe ta zama tawa! Sabuwar Range Rover kirar 2023."

Asali: Legit.ng

Online view pixel