‘Yan Bindigan da Suka Dauke Fasinjojin Jirgin Kasa na Shirin Aure ‘Yar shekara 21

‘Yan Bindigan da Suka Dauke Fasinjojin Jirgin Kasa na Shirin Aure ‘Yar shekara 21

  • Akwai wata yarinya ‘yar shekara 21 daga cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna da aka tare a hanya a karshen watan Maris
  • Alhaji Tukur Mamu yace wannan Budurwa mai suna Azurfa Lois John ta na cikin barazana, domin ‘yan ta’adda na neman ta da aure
  • A wata sanarwa da ya fitar, Mamu ya ankarar da Gwamnati, ya nemi a kubutar da wannan yarinya kafin ta zama matar ‘yan ta’adda

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Tukur Mamu ya bada sanarwar cewa ‘yan bindiga na shirin auren wata daga cikin fasinjojin jirgin da aka sace a hanyar Abuja-Kaduna.

The Cable ta ce Alhaji Tukur Mamu wanda na-kusa ne da Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana haka a ranar Juma’a, 19 ga watan Agusta 2022.

Yayin da yake bada sanarwar sakin wasu mutane hudu a jiya, ‘dan jaridar ya fadakar da mutane cewa ‘yar autar da ke tsare ta na fuskantar barazana.

Kara karanta wannan

Mazauna a Kaduna sun fusata, sun sheke wata wata mai boye 'yan bindiga a gidanta

Azurfa Lois John ita ce mai mafi karancin shekaru a matafiyan da aka dauke a jirgin kasan Abuja-Kaduna a watan Maris, kusan watanni biyar yau.

This Day tace Mamu ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kungiyar kiristoci da suyi kokarin ganin an kubutar da wannan yarinya kafin a aure ta.

Sanarwar Tukur Mamu

“Wannan sako ne ga gwamnatin tarayya da kuma kungiyar kiristoci na CAN, bayanan da samu sun tabbatar mani idan ba a fito da ‘yar autar fasinjojin jirgin kasan da aka dauke ba, Azurfa Lois John, ‘yar shekara 21, lallai wadanda suka dauke su za su yi irin abin da ya faru da Leah Sharibu, su na kokarin auren ta ba da dadewa ba."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

- Tukur Mamu

Fasinjojin Jirgin Kasa
Buhari da 'Yanuwan wadanda aka sace Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Mawallafin na Desert Herald yace wani daga cikin manyan dakarun ‘yan ta’adda ne yake soyayya da Azurfa John, yake kuma burin ya zama mijin ta.

Kara karanta wannan

Majalisa Na Binciken Ministoci, An Bada Kwangilar Share Daji a Naira Biliyan 18.6

Ka da a sake yin na Leah Sharibu

“Duk da na san fitar da wannan labari zai tada hankalin ‘yanuwanta da masoyanta, amma daukacin ‘Yan Najeriya na bukatar gujewa maimaituwar irin abin da ya faru da Leah Sharibu.”
“Ina kira ga musamman CAN, ka da ta siyasantar da wannan lamarin ko ta dauke shi a matsayin soki-burutsu kamar yadda aka yi a baya.
“Ayi aiki da hukumomin da suka dace domin a kubutar da ita tun kafin lokaci ya kure.”

- Tukur Mamu

Kamar yadda aka rahoto a Premium Times, Mamu ya yi addu’a gwamnatin tarayya ta iya kubutar da ragowar wadanda suke hannun wadannan ‘yan ta’adda.

'Yar shekara 90 ta fito

A jiya aka samu labarin an kubutar da Mama Halimatu Atta mai shekara 90 da kuma ‘diyarta, Hajiya Adama Atta Aliyu bayan sun yi kwanaki 144 a cikin jeji.

Sauran wadanda aka fito da su jiya su ne: Mohammed Sani Abdulmaji (M.S Ustaz) da Modin Modi Bodinga.

Kara karanta wannan

Shawari kyauta: Hanyoyi 15 da za ku bi domin kiyaye kanku daga fadawa matsala a Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel